Taron NEC: Kungiyar Gwamnonin PDP Ta Fadi Gaskiya kan Shigar da Kara Kotu
- Gwamnonin PDP sun karyata rahoton da ke bayyana cewa sun shigar da korafi a gaban kotun tarayya kan rikicin jam'iyyar
- Kungiyar gwamnonin karkashin jagorancin gwamnan Bala Muhammad ta zargi masu son hada rikici da fitar da labarin
- Wannan na zuwa ne bayan jam'iyyar ta fitar da sanarwar dage babban taronta na kasa da aka sanya zai gudana a watan Oktoba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Zamfara - Shugaban gwamnonin PDP kuma gwamnan Bauchi, Bala Muhammad ya yi martani kan zargin shigar da kara gaban kotu kan babban taron PDP na NEC.
Martanin ya biyo bullar wani labari cewa kungiyar gwamnonin ta shigar da kara babbar kotu da ke Gusau, ta na neman a bari su gudanar da taron kwamitin zartarwar PDP.
A sakon da kungiyar ta wallafa a shafinta na X, kungiyar gwamnonin ta barranta kanta da rahoton, tare da bayyana cewa babu kamshin gaskiya a cikinta.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnonin PDP sun musanta zuwa kotu
Jaridar The Nation ta tattaro cewa gwamnonin PDP sun nuna rashin jin dadin rahoton da ke bayyana cewa sun shigar da kara kotu kan babban taron jam'iyyar.
Kungiyar gwamnonin, karkashin gwamna Bala Muhammad ta ce babu wanda aka sa ya shigar da kara a madadinta na neman tilasta babban taron jam'iyyar na kasa.
Gwamnonin PDP sun shawarci yan Najeriya
Kuniyar gwamnonin PDP a kasar nan ta nemi jama'a da magoya bayanta da su yi watsi da rahoton da ke danganta su da daukar matakin shari'a kan dambarwar PDP.
Kungiyar ta zargi wandanda su ka wallafa labarin da cewa su na son bata wa gwamnan Bauchi, kuma shugaban kungiyar suna ne a idon jama'a.
Jam'iyyar PDP ta dage taron NEC
A baya mun ruwaito cewa jam'iyyar PDP ta sake bayyana dage babban kwamitin zartarwa na jam'iyyar zuwa watan Nuwamba, yayin da ake kokarin magance rikicin da ta addabe ta.
Gwamnan jihar Bauchi, kuma shugaban kungiyar gwamnonin PDP na kasa, Bala Muhammad ne ya bayyana dage taron da aka shirya gudanarwa a ranar 24 Oktoba, 2024.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng