Tsohon Gwamna Shekarau Ya Fadi Dalilin Ɗauko Sabuwar Tafiyar Siyasa a Arewa

Tsohon Gwamna Shekarau Ya Fadi Dalilin Ɗauko Sabuwar Tafiyar Siyasa a Arewa

  • Tsohon gwamnan Kano, Ibrahim Shekarau ya nuna cewa sabuwar tafiyarsu na son zaburar da jama'a kan shugabanci na gari
  • Tsohon gwamnan ya fadi haka ne bayan ziyarar da ya kai Abeokuta domin zama da tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo
  • Malam Ibrahim Shekarau ya ce kasar nan, musamman Arewa da su ka fito na fama da matsaloli da ke bukatar a magance su

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano - Tsohon Sanata, kuma toshon gwamnan Kano sau biyu, Malam Ibrahim Shekarau bayyana shirinsu na zaburar da yan kasar nan kan zaben shugabanni na gari.

Ya bayyana haka ne a jihar Legas jim kadan bayan wata ziyarar kara hada gangamin sabuwar tafiyarsu ta 'League of Northern Democrats.'

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya gana da gwamna kan mutuwar mutane 181, bayanai sun fito

Shekarau
Malam Ibrahim Shekarau na jagorantar samar da shugabanci na gari Hoto: Muhammad Ath-thaaniy
Asali: Facebook

Jaridar RFI ta tattaro cewa Malam Ibrahim Shekarau ya jagoranci tawaga ta musamman zuwa ganin tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo a gidansa da ke Abeokuta.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dalilin tawagar Shekarau na ziyartar Obasanjo

Tsohon gwamnan Kano, Malam Ibrahim Shekarau ya ce sun ziyarci tsohon shugaban kasa a mulkin soja da na farar hula, Olusegun Obasanjo domin neman shawarwari.

Jaridar Solacebase ta tattaro cewa yayin ziyarar, Shekarau ya ce sabuwar tafiyarsu na da mutane akalla 400 masu ra'ayin ciyar da Arewa da Najeriya gaba.

Shekarau ya koka da matsalolin Najeriya

Tsohon Sanata, Malam Ibrahim Shekarau ya ce akwai matsalolin da su ka yi wa sassan kasar nan, musamman Arewa katutu.

"Akwai matsaloli da yawa da ke damunmu: rashin tsaro, rashin hadin kai a tsakaninmu da matsalolin ilimi," cewar Ibrahim Shekarau.

Ya ce ba wai su na ganin sun fi kowa ba ne a kasar nan, amma akwai kyakkyawan zaton wadanda ke cikin tafiyar masu nagarta ne.

Kara karanta wannan

Taron NEC: Rikicin PDP ya ɗauki sabon salo, gwamna ya jagoranci kai ƙara kotu

Shekarau ya ki shiga rikicin masarautar Kano

A baya mun ruwaito cewa bayan bayyana dalilin rashin cewa komai kan rikicin masarautar Kano, Sanata Ibrahim Shekarau ya bayyana takaici kan yadda lamarin ke kara ta'azzara.

Malam Ibahim Shekarau ya ce bai ce uffan kan rikicin ba ne saboda magana na gaban kotu, amma ya yi fatan za a cimma matsaya wajen waraware dambarwar masarautar da wuri.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.