Ta Faru Ta Kare, Kotu Ta Tsige Shugaba da Manyan Jami'an Hukumar Zaben Jihar Kano
- Wata babbar kotun tarayya ta kori shugaban hukumar zaben jihar Kano, Farfesa Sani Malumfashi daga kan kujerarsa
- Hakazalika, kotun ta kori wasu daga cikin manyan jami'an hukumar zaben saboda kasancewarsu 'yan jami'iyyar NNPP
- Babbar kotun ta kuma haramtawa KANSIEC gudanar da zaben kananan hukumomin sai an nada sababbin shugabanni
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Kano - Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Kano ta tsige shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar Kano (KANSIEC), Farfesa Sani Malumfashi.
A hukuncin da ta yanke a ranar Talata, kotun ta tsige Farfesa Sani Malumfashi saboda kasancewarsa dan jam’iyyar NNPP a hukumance.
Aminu Tiga da jam’iyyar APC ne suka shigar da karar, kamar yadda rahoton jaridar The Nation ya nuna.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kotu ta yi hukunci kan karar APC
Wadanda ake karar dai sun hada da babban lauyan gwamnati kuma kwamishinan shari’a na jihar, Haruna Dederi da wasu mutum 14.
Da yake yanke hukunci, Mai shari’a S.A Amobede, ya kuma ce Kabir Zakirai, sakataren hukumar ba ma’aikacin gwamnatin jihar Kano ba ne.
Alkalin kotun ya ce Zakirai bai cancanci a nada shi mukamin ba kamar yadda sashe na 14 na dokar hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar Kano ta shekarar 2001 ta tanada.
“An rusa duk abin da wanda ake tuhuma na takwas ke yi a shirye-shiryen zaben kananan hukumomin jihar Kano a shekarar 2024 kuma shirin ba shi da wani tasiri."
- A cewar kotun.
Kano: An tsige shugabannin KANSIEC
Mai shari'a S.A Amobede ya ci gaba da cewa:
"Da wannan, kotu ta rusa nadin wadanda ake kara na 8 zuwa na 14 ba tare da bata lokaci ba kuma an kore su daga mukamansu na shugaba da jami'an hukumar.
“An hana su gudanar da zaben kananan hukumomi 44 na jihar Kano da aka shirya yi a 2024 har sai an nada wadanda suka cancanta."
Ya kuma umurci ‘yan sanda da sauran hukumomin tsaro da su gaggauta tabbatar da cika sharuddan sashe na 197 (1) (b) da 199 (2) da 200 (1) (a) na kundin tsarin mulkin Najeriya.
Kotu ta hana zaben ciyamomin Kano
Tun da fari, mun ruwaito cewa wata babbar kotun tarayya ta dakatar da hukumar zabe mai zaman kanta a Kano daga gudanar da zaben ƙananan hukumomi.
Mai shari’a S.A Amobede ya yanke hukuncin cewa nada Farfesa Sani Malumfashi matsayin shugaban hukumar zaben alhalin yana cikin NNPP ya saba doka.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng