Babbar Kotu Ta Yanke Hukunci kan Zaben Kananan Hukumomin da Za a Yi a Kano
- Babbar kotun tarayya ta hana zaɓen ƙananan hukumomin da ake shirin yi a Kano ranar Asabar, 26 ga watan Oktoba, 2024
- Alkalin kotun, Simon Ameboda ya ce naɗn ƴan jam'iyyar NNPP a matsayin shugabannin hukumar zaɓen Kano ya saɓa doka
- Mai Shari'a ya kuma umarci hukumar zaɓe ta ƙasa watau INEC kada ta ba Kano kayan zaɓe har sai an gyara naɗe-naɗen KANSIEC
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Kano - Babbar kotun tarayya mai zama a Kano ta hana gudanar da zaɓen kananan hukumomin da aka shirya yi ranar Asabar mai zuwa.
Alkalin kotun Mai Shari'a Simon Ameboda ne ya yanke wannan hukuncin a zaman yau Talata, 22 ga watan Oktoba, 2024.
Meyasa kotu ta hana zaɓen Kano?
Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito, alkalin ya ce naɗin shugaban hukumar zaɓen Kano da sauran ƴan kwamitin gudanarwa ya saɓa tanadin kundin tsarin mulki.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mai shari'a Ameboda ya ce naɗin ƴan jam'iyyar NNPP a matsayin waɗanda za su tafiyar da hukumar KANSIEC ya saɓawa sashe na 197(1) da sashe na 200(1) na kundin tsarin mulki na 1999.
Haka nan kuma ya saɓawa sashe na 4(b) na kundin dokokin hukumar zaɓe mai zaman kanta ta jihar Kano 2001.
Kotu ta hana INEC ba da kayan zaɓe a Kano
Kotun ta bayyana cewa a yadda hukumar KANSIEC take a halin yanzu, ba za ta iya gudanar da sahihin zaɓen kananan hukumomi ba a Kano, rahoton Guardian.
Bugu da ƙari, babbar kotun tarayya ta umarci hukumar zaɓe mai zman kanta INEC da kada ta ba KANSIEC kayayykin zaɓe har sai an gyara shugabancinta.
Hukumar KANSIEC dai ta shirya gudanar da zaɓen ciyamomi da kansiloli a faɗin kananam hukumomi 44 da ke Kano ranar Asabar, 26 ga watan Oktoba.
NNPP ta ƙara rasa jiga-jiganta a Kano
A wani rahoton kuma jam'iyyar NNPP ta sake samun koma baya a jihar Kano bayan wasu jagororinta sun sauya sheƙa zuwa APC mai adawa.
Jagororin jam'iyyar NNPP da suka sauya sheƙa zuwa APC sun fito ne daga ƙananan hukumomin Tofa da Dawakin Tofa na Arewacin Kano.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng