'Kirista Dan Kudu,' Tsagin PDP Ya Fadi Wanda Zai Shiga Takara a 2027

'Kirista Dan Kudu,' Tsagin PDP Ya Fadi Wanda Zai Shiga Takara a 2027

  • Wasu yan jam'iyyar PDP da ke biyayya ga ministan Abuja, Nyesom Ezonwo Wike sun fara shirin waje da Atiku Abubakar a zaben 2027
  • Yan PDP da ke bangaren Nyesom Wike sun fara magana kan yiwuwar marawa gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde baya maimakon Atiku
  • Haka zalika sun yi magana a kan yiwuwar dawowar dan takarar jam'iyyar Labour, Peter Obi zuwa PDP domin zabe mai zuwa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Rahotanni na nuni da cewa rikicin jam'iyyar PDP na kara ƙamari kan zaben shekarar 2027.

Wasu yan PDP masu biyayya ga mnistan Abuja, Nyesom Ezonwo Wike sun fara shirin juya baya ga Atiku Abubakar a 2027.

Kara karanta wannan

"Ka da zaben Edo ya rude ka": PDP ta ja kunnen Ganduje kan kwace yankin Tinubu

Atiku
Tsagin PDP zai juya baya ga Atiku a 2027. Hoto: Atiku Abubakar|Nyesom Wike
Asali: Facebook

Jaridar Punch ta fitar da rahoto kan wanda wasu yan PDP suke so ya tsaya takara a 2027 da yadda za su samar masa da mataimaki daga Arewa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

2027: 'Yan PDP za su juyawa Atiku baya

Wasu manya a PDP da suke goyon bayan Wike sun fara maganar tsayar da gwamnan Oyo, Seyi Makinde takarar zaɓe a 2027.

A makon da ya wuce gwamna Seyi Makinde ya bayyana cewa ya cancanta ya tsaya takarar zaɓen shugaban kasa a Najeriya.

Dalilin yakar Atiku Abubakar a PDP

Wani jigo a PDP da ya bukaci a ɓoye sunansa ya bayyana cewa ba za su yarda wani mutum (Atiku) ya rika gwada sa'a a jam'iyyar ba duk bayan shekaru hudu.

Jigon jam'iyyar ya ce za su mara baya ga gwamna Seyi Makinde saboda shi matashi ne kuma Kirista dan Kudu wanda zai iya karawa da Bola Tinubu.

Kara karanta wannan

Rigimar APC ta sake dagulewa da Sanata Wamakko da Lamido suka ja ɓangarensu

Haka zalika kusa a PDP ya ce suna tsoron cewa Atiku Abubakar ba zai samu karɓuwa wajen masu zabe ba a 2027 kamar yadda Legit ta ruwaito.

Maganar shigar Peter Obi PDP

Wani dan kwamitin zartarwar jam'iyyar PDP ya ce har yanzu Peter Obi yana LP kuma bai yanke matsayar sauya-sheka ba.

Hadimin Atiku Abubakar a harkokin yada labarai, ya ce ba su jin tsoron tsayawar wani takara amma a yanzu sun mayar da hankali ne kan fitar da yan Najeriya daga matsin tattalin arziki.

SDP ta yi magana kan hadaka a 2027

A wani rahoton, kun ji cewa tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa a inuwar SDP, Adewole Adebayo ya ce dole a samu manufa ɗaya idan za a haɗe a zaɓen 2027.

Ya ce gwamnatin Bola Tinubu da ta Muhammadu Buhari sun isa zama misalin haɗaka ba tare da manufa ba sai kwaɗayin mulki.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng