"Ka da Zaben Edo Ya Rude Ka": PDP Ta Ja Kunnen Ganduje kan Kwace Jihohin Yarbawa
- Ana shirin zaben Ondo, jam'iyyar PDP ta ja kunnen shugaban APC, Abdullahi Ganduje kan zaben da za a yi a Nuwamba
- Jam'iyyar PDP ta gargadi Ganduje kan kalamansa da ya ce za su kwace dukan jihohin Kudu maso Yamma a Najeriya
- PDP ta ja kunnen Ganduje da ya yi hankali da yankin saboda sun waye a siyasa ba kamar Edo ba ne da za a siye su
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Jam'iyyar PDP ta mayar da martani ga Abdullahi Ganduje kan kwace yankin Kudu maso Yamma.
Jam'iyyar PDP ta ce yankin Kudu maso Yamma ba kamar jihar Edo ba ne inda ya ce ka da zaben Edo ya yaudare su.
Ganduje ya sha alwashin kwace yankin Yarbawa
Sakataren jam'iyyar, Debo Ologunagba shi ya tura wannan gargadi a jiya Litinin 21 ga watan Oktoban 2024, cewar rahoton Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ologunagba ya ce yankin Kudu maso Yamma ba kamar Edo ba ne da za a kwace ko siya a zabe kamar yadda APC ke yi.
Wannan martani na zuwa ne bayan Ganduje ya sha alwashin cewa APC za ta kwace duka jihohin yankin guda shida.
Ganduje ya fadi haka ne a birnin Akure da ke jihar Ondo a ranar Lahadi 20 ga watan Oktoban 2024 yayin jawabinsa.
Jam'iyyar APC na rike da jihohin Lagos da Ekiti da Ondo da kuma Ogun inda PDP ke jagorancin Oyo da Osun.
PDP ta ja kunnen Ganduje kan zaben Ondo
Sai dai jam'iyyar PDP ta yi martani ga Ganduje inda ta ce kalamansa shiririta ne kawai da rashin tsari, cewar Vanguard.
"Wannan gargadi ne, mutanen yankin Kudu maso Yamma wayayyu ne a siyasa sun san abin da suke so."
"Kamar yadda Ganduje ya je Ondo ya ke fadan abin ba su dace ba, wannan barazana ne ga dimukraɗiyya."
"Ya kamata ya yi hankali da yankin, zaben Ondo ba irin wanda ya saɓa gani ba ne, yan jihar sun shirya tsaf domin zaben PDP."
- Debo Ologunagba
Ganduje ya musanta shirin neman kujerar Tinubu
Kun ji cewa Shugaban APC Abdullahi Ganduje ya musanta raɗe-raɗin yana shirin tsayawa takarar shugaban ƙasa a babban zaɓen 2027.
Ganduje ya ce fastocin da ke yawo a Abuja ba su da alaƙa da shi kuma ya yi zargin akwai hannun wasu ƴan Kwankwasiyya a ciki.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng