PDP Ta Shirya Korar Tsohon Gwamnanta bayan Nuna Goyon Baya ga Gwamnan APC
- Jam'iyyar PDP a jihar Ekiti ta gabatar da rahoto bayan binciken tsohon gwamnan jihar, Ayodele Fayose
- Jam'iyyar ta ce ta ba kwamitin ladabtarwa shawara kan korar Fayose daga jam'iyyar kan zargin cin dunduniyarta
- Hakan ya biyo bayan zargin Fayose da goyon bayan Gwamna Biodun Oyebanji na APC a jihar Ekiti ƙarara
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Ekiti - Jam'iyyar PDP tana shirin korar tsohon gwamnan Ekiti, Mr. Ayodele Fayose daga cikinta.
Reshen jam'iyyar da ke Ekiti tana duba yiwuwar dakatar da Fayose kan cin dunduniyarta da yake yi.
Jam'iyyar PDP ta shirya sallamar tsohon gwamna
Mukaddashin shugaban jam'iyyar, Dare Adeleke shi ya bayyana haka a yau Lahadi 20 ga watan Oktoban 2024, cewar The Nation.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Adeleke ya ce sun dauki matakin ne bayan gudanar da bincike tare da mika rahoto ga kwamitin ladabtarwa na jam'iyyar.
Ya ce daga cikin zarginsa da ake yi akwai cin amanar jam'iyyar da rashin mutunta muradunta, The Guardian ta ruwaito.
Har ila yau, Adeleke ya ce babban zunubinsa shi ne goyon bayan Gwamna Biodun Oyebanji na APC a jihar Ekiti.
PDP ta gargadi al'umma kan aminta da Fayose
Shugaban PDP ya ce abubuwan da Fayose ke yi na jawo musu abin kunya da kuma yaudarar mambobin jam'iyyar.
"Muna mai tabbatar muku da cewa Fayose ba dan PDP ba ne, duk abin da ya fada ya yi ne domin farantawa mai gidansa, Gwamna Biodun Oyebanji."
"Babu mai daukar Fayose da muhimmanci saboda komai yana yi ne saboda abin da kawai zai samu."
- Dare Adeleke
Kanin Fayose ya ayyana kansa shugaban PDP
A wani labarin, kun ji cewa rigimar jam'iyyar PDP ta sauya salo bayan kanin tsohon gwamnan Ekiti, Ayodele Fayose ya ayyana kansa shugabanta.
Kanin tsohon gwamnan Ekiti mai suna Isaac Fayose ya ce daga yau shi ne shugabanta duk wanda ba yarda ba ya je kotu.
Hakan ya biyo bayan rikicin da ya barke a PDP da ke neman raba ta gida biyu bayan tsaginta ya dakatar da shugabanta, Umar Damagum.
Asali: Legit.ng