'Sai An Kula Kashi': Atiku Ya Yi wa Ministan Tinubu, Wike Wankin Babban Bargo

'Sai An Kula Kashi': Atiku Ya Yi wa Ministan Tinubu, Wike Wankin Babban Bargo

  • Kalaman da ministan birnin tarayya, Barista Nyesom Wike ya yi a wani taro a Fatakwal, jihar Ribas sun fusata Atiku Abubakar
  • A wani martani da Atiku ya yiwa Wike, ya ce ba zai iya kaskantar da kansa ya koma kamar Wike ba wanda ya siyasantar da komai
  • Atiku ya ce ya damu da halin da 'yan Najeriya ke ciki sabanin Wike da shiga gidajen talabijin yana karya da kare gwamnatin APC

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya ce ba zai iya kaskantar da kansa zuwa matsayin da ministan birnin tarayya, Barista Nyesom Wike ya ke ba.

Atiku ya zargi Wike da siyasantar da kuncin rayuwa da tsadar da 'yan Najeriya ke fuskanta a karkashin gwamnatin Bola Tinubu.

Kara karanta wannan

'Yan Najeriya ba son ka suke ba: Wike ya yiwa Atiku bankada a wurin taro, ya caccake shi

Atiku ya yi martani ga kalaman da Wike ya yi a wani taron Fatakwal
Atiku ya caccaki Wike, ya ce ya damu da halin da 'yan Najeriya ke ciki. Hoto: @atiku, @GovWike
Asali: Facebook

Me ya jawo Atiku ya soki Wike?

Mun ruwaito cewa Wike, da yake magana a wani taro a Fatakwal a ranar Asabar, ya bayyana Atiku a matsayin dan siyasar da aka dawo daga rakiyarsa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ministan ya yi martani ne ga kalaman Atiku bayan zaben ciyamomin Ribas, inda shin (Atiku) ya bayyana cewa yanzu haka 'yan jihar sun daina jin tsoron barazanar Wike.

Wike ya nuna cewa APC ba ta shiga zaben Ribas ba don haka ba laifi ba ne don ba ta samu nasara ba, amma Atiku ya yi zabe a 2023 wanda 'yan kasar suka ki zabarsa.

Atiku ya caccaki ministan Abuja

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa Atiku Abubakar, ta bakin Mista Paul Ibe, mai ba shi shawara kan harkokin yada labarai ya ce:

"Idan har Nyesom Wike ya yarda cewa komai na tafiya daidai a gwamnatin da ya ke yiwa aiki, to hakan ya nuna ba jama'a ne a gabansa ba, bukatarsa ce ya saka a gaba.

Kara karanta wannan

'Yana yawo cikin dare,' Sanata ya tona yadda Tinubu yake zagaya gari a boye

"Yayin da Wike ya karkata wajen shiga gidajen talabijin yana yada karya da kare gwamnati, mu muna damu da halin da al'ummar kasar ke ciki.
"Burinmu shi ne ci gaban al'ummar Najeriya don haka ba za mu kaskantar da kanmu kamar yadda ya yi ba, za mu jajurce domin ganin mutane sun samu walwala."

Rigimar Atiku da Wike ta tsananta

A wani labarin, mun ruwaito cewa dangantaka na kara tsami tsakanin Atiku Abubakar da ministan birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, kan shugabancin jam'iyyar PDP.

An ce tsohon mataimakin shugaban kasar yana goyon bayan Gabriel Suswam ya zama shugaban PDP yayin da Wike ke goyon bayan Umar Damagum.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.