Kogi: An Sanar da Sakamakon Zaben Kananan Hukumomi, Mace Tilo Ta Samu Kujera

Kogi: An Sanar da Sakamakon Zaben Kananan Hukumomi, Mace Tilo Ta Samu Kujera

  • Yayin da ake dakon sakamakon zaben kananan hukumomi a Kogi, hukumar zabe a jihar ta raba fada tsakanin jam'iyyu
  • Shugaban hukumar zaben a jihar, KSIEC, Mamman Nda Eri shi ya bayyana sakamakon a jiya Asabar 19 ga watan Oktoban 2024
  • Eri ya tabbatar da cewa jam'iyyar APC mai mulkin jihar ita ta lashe dukan kujerun ƙananan hukumomin da na kansiloli

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kogi - Hukumar zaben jihar Kogi (KSIEC) ta sanar da zaben kananan hukumomi 21 da aka gudanar.

Hukumar ta tabbatar da cewa jam'iyyar APC mai mulkin jihar ta lashe dukan kujerun ƙananan hukumomi da kuma kansiloli 239 da aka yi.

Kara karanta wannan

Sunayen wadanda za su zama sababbin shugabannin kananan hukumomin Kaduna

An sanar da sakamakon zaben kananan hukumomi a jihar Kogi
Hukumar zaben jihar Kogi ta sanar da zaben kananan hukumomi. Hoto: Ahmed Usman Ododo.
Asali: Facebook

Kogi: APC ta lashe zaben kananan hukumomi

Shugaban hukumar, Mamman Nda Eri shi ya tabbatar da haka a daren jiya Asabar 19 ga watan Oktoban 2024, cewar PM News.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Eri wanda ya ce APC ce ta yi nasarar lashe dukan kujerun amma abin mamaki bai ba da bayanai kan yawan kuri'un da ta samu ba.

Sai dai kawai ya fadi sunayen wadanda suka yi nasara ciki har da mace a karamar hukumar Ogori-Magongo ba tare da fadin yawan kuri'u da aka kada ba da wadanda suka lalace.

Shugaban hukumar ya yabawa al'umma, jami'an tsaro

Shugaban hukumar ya fayyace yadda kowane wakilin zabe ya sanar da sakamakon tun daga rumfuna har zuwa kananan hukumomi a fadin jihar, cewar TheCable.

Daga bisani, Eri ya godewa al'ummar jihar da jami'an tsaro da kuma ma'aikatan hukumar kan jajircewarsu wurin tabbatar da yin zaben cikin lumana ba tare da matsala ba.

Kara karanta wannan

Kananan hukumomi: Yan sanda sun tarwatsa matasa, an fadi halin da ake ciki a Kaduna

Kaduna: APC ta lashe zaben kananan hukumomi

Mun baku labarin cewa hukumar zaɓen jihar Kaduna (KAD-SIECOM) ta sanar da zaɓen shugabannin ƙananana hukumomin da aka gudanar a ranar Asabar.

Shugabar hukumar zaɓen, Hajara Mohammed ta bayyana cewa jam'iyyar APC mai mulki ta lashe dukkanin kujerun ciyamomi 23 a zaɓen.

Hajara ta kuma sanar da cewa APC mai mulkin jihar ta lashe kujerun kansiloli 255 a zaɓen wanda jam'iyyun siyasa takwas suka fafata.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.