'Yan Najeriya Ba Son Ka Suke Ba: Wike Ya Yiwa Atiku Bankada a Wurin Taro, Ya Caccake Shi

'Yan Najeriya Ba Son Ka Suke Ba: Wike Ya Yiwa Atiku Bankada a Wurin Taro, Ya Caccake Shi

  • Nyesom Wike, tsohon gwamnan Rivers ya yiwa Atiku Abubakar wankin babban bargo a wurin wani taro
  • An ruwaito yadda Atiku ya yabawa gwamna Fubara bisa jagorantar zaben kananan hukumomi cikin aminci
  • Akwai tsama tsakanin Atiku da Wike tun bayan da Wike ya rasa tikitin takarar shugaban kasa a PDP a 2023

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Jihar Rivers - Ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike, ya caccaki tsohon mataimakin shugaban kasa kuma dan takarar shugaban kasa a zaben 2023 a PDP, Atiku Abubakar.

A baya kadan, Atiku ya yabawa gwamna Siminalayi Fubara na jihar Rivers, bisa jajircewarsa wajen kare muradun jama’arsa, rahoton Punch.

A martanin Atiku ga zaben da aka gudanar na kananan hukumomi a jihar, ya ce tabbas jihar Rivers na hannun na gari, kuma za a ci gaba da tafiyar da tsarin dimokradiyya ba tare da tangarda ba.

Kara karanta wannan

"Har yanzu yana jin raɗaɗin 2023," Jigon PDP ya kwancewa tsohon gwamna zani a kasuwa

Atiku ya sha caccaka a hannun Wike
Yadda Wike ya caccaki Atiku kan siyasa | Hoto: Atiku Abubakar, Nyesom Wike
Asali: Facebook

Wike ya yiwa Atiku wankin babban bargo

Da yake martani yayin wata liyafar cin abinci na karrama majalisar jihar Rivers karo na 10 a ranar Asabar, Wike ya yi ikirarin cewa Atiku ya rasa nasaba da siyasar kasar nan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya kara da cewa ‘yan Najeriya sun ki jinin Atiku, bayan da ya tsaya takara a zaben shugaban kasa kuma ya fadi “sau da yawa” a tarihin siyasarsa, Daily Trust ta ruwaito.

“Ba mu taba tsayawa takara a zaben kananan hukumomi ba. Mun taba takara? Mun karbi fom?
“Ina jin Atiku Abubakar yana cewa, ‘Kai, wai sun yi watsi dani a Jihar Ribas.’ To, idan aka ce, ko da yake bai yarda ba, ya yi rashin nasara sau da yawa, ‘yan Najeriya ma sun ki shi kenan.
“Idan ka ce zaben da ba mu yi takara ba, ba mu taba shiga ba, hakan ya nuna ‘yan Najeriya sun ki mu, to, ku da kuka yi takara kuma kuka yi rashin nasara fa, ’yan Najeriya sun yi watsi da ku kenan, don haka ku tattara kayan ku ku koma gida.”

Kara karanta wannan

'Za su hana Tinubu takara a 2027?' Kusa ya dura kan masu sukar Atiku

Kitimurmurar da ke tsakanin Atiku da Wike

Atiku da Wike dai sun nemi tikitin takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar PDP a zaben 2023.

Sai dai, Wike ya yi rashin nasara a zaben fidda gwani, inda Atiku ya zabi Okowa a matsayin abokin takararsa, lamarin da ya bata tsakaninsu.

Duk kokarin sulhunta su ya ci tura kuma a karshe Wike ya yi wa shugaba Bola Tinubu aikin bayan fage har ta kai ga faduwar Atiku a zaben.

Alamu masu karfi sun nuna cewa, an yiwa Wike tukuici ne da kujerar minista a gwamnatin Tinubu bisa aikinsa na zaben 2023.

Meye alakar Wike da jam'iyyar APC?

A bangare guda, shugaban APC a Ribas, Dakta Tony Okocha, ya bayyana cewa ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike ba dan jam’iyyarsu ba ne.

A cewarsa, Nyesom Wike ba zai taba barin jam’iyyar adawa ba, yana mai cewa, “ya dade yana cewa PDP ta yi masa gata, ba zai bar ta ba."

Jaridar Punch ta rahoto Tony ya jaddada maganarsa ta cewa ministan babban birnin tarayya ba zai taba fita daga jam'iyyar PDP ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.