2027: Mutane 7 da Suka Fara Shinshina Kujerar Shugaba Bola Tinubu Tun Yanzu

2027: Mutane 7 da Suka Fara Shinshina Kujerar Shugaba Bola Tinubu Tun Yanzu

Abuja - Tun kafin Bola Ahmed Tinubu ya ci rabin wa’adinsa, wasu sun fara kawo zancen wadanda za su nemi mulki a zaben 2027.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Legit Hausa ta bibiyi siyasar Najeriya, ta kawo sunayen wasu manyan ‘yan siyasan da ake ganin za su iya yin takarar shugaban kasa.

Bola Tinubu
A 2027, Bola Tinubu zai fuskanci adawa a Najeriya Hoto; Getty Images
Asali: Getty Images

'Yan siyasar da za su iya gwabzawa da Tinubu

1. Atiku Abubakar

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Har yanzu magoya bayan Atiku Abubakar su na cigaba da kira a gare shi da ya sake jarraba sa’arsa, ya kuma tsayawa takara a 2027.

Ana da labara ‘yan siyasa kamar Ayo Fayose sun fara nunawa tsohon mataimakin shugaban kasar cewa ba za su mara masa baya ba.

Kara karanta wannan

‘Yan APC da suka koma kuka da gwamnati saboda tsadar rayuwa a zamanin Tinubu

2. Peter Obi

Kamar PDP da sauran manyan jam’iyyun hamayya, ana fama da rikici a LP amma wannan bai kashewa masoyan Peter Obi kwarin guiwa ba.

A shafukan sada zumunta, ana ganin yadda ake cigaba da nunawa Obi kauna. ‘Dan siyasar ya saba fada cewa bai dauki takara dole ba.

3. Rabiu Kwankwaso

Kwanan nan aka rahoto Rabiu Kwankwaso ya sukar jam’iyyun PDP da APC, ya na mai cika-bakin cewa mutane za su zabi NNPP a 2027.

Duk da jam’iyyarsa ba ta kai labara a zaben da ya gabata ba, alamu na nuna ‘dan siyasar bai cire ran zama shugaban Najeriya kwanan nan ba.

4. Seyi Makinde

Wani ‘dan siyasa daga Kudu maso yamma da aka fara jifa da zancen takarar shugaban kasa shi ne gwamnan jihar Oyo watau Seyi Makinde.

An rahoto Seyi Makinde ya na maida martani da cewa idan lokacin ya yi zai yi magana. A 2027 zai cika wa’adinsa na shekaru takwas a Ibadan.

Kara karanta wannan

Malaman musulunci 5 da za su iya goyon bayan Tinubu idan ya nemi tazarce a 2027

5. Orji Uzor Kalu

Sanata Orji Uzor Kalu mai wakiltar Arewacin Abia a majalisar dattawa ya fito karara ya na fadawa duniya yana sha’awar neman mulkin kasa.

Orji Uzor Kalu wanda babban ‘dan siyasa ne ya taba tsayawa takarar shugaban kasa a jam’iyyar PPA a 2007, Ummaru Yar’adua ya doke shi.

6. Bala Mohammad

Tun a zaben 2023, Bala Mohammad ya fara nunawa Najeriya zai yi sha’awar zama shugaban kasa, ya nemi tikitin PDP amma bai dace ba.

Kamar Seyi Makinde, Gwamnan na jihar Bauchi zai bar ofis ne a 2027 don haka babu mamaki shi da magoya bayansa su sake shiga takara.

7. Goodluck Jonathan

Kwanan aka Tribune ta fitar da labari cewa akwai wasu ‘yan siyasar da ke kokarin ganin an tsaida Goodluck Jonathan takara a zabe mai zuwa.

Watakila masu wannan shiri su na tunanin Jonathan zai samu karbuwa idan ya gwabza da Bola Tinubu wanda ake ganin zai nemi tazarce

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng