Jerin Sunayen Wadanda Za Su Zama Sababbin Shugabannin Kananan Hukumomin Kaduna

Jerin Sunayen Wadanda Za Su Zama Sababbin Shugabannin Kananan Hukumomin Kaduna

  • An yi zabe a kananan hukumomin Kaduna kuma an tabbatar da wadanda za su zama ciyomomin jihar
  • Bayan shugabannin kananan hukumomi, KADSIECOM ta sanar da APC ta lashe duka kujerun kansiloli 255
  • Legit ta yi kokarin jero sunayen duka wadanda suka lashe zaben kananan hukumomin a karkashin APC

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Kaduna - An kammala gudanar da zaben kananan hukumomi a jihar Kaduna, kuma an tabbatar da nasarar APC mai-ci.

Hukumar zabe mai zaman kanta a jihar Kaduna (KADSIECOM) ta ce APC ta samu duka ciyomomi 23 da kuma kansiloli 255.

Kaduna
APC ta cinye zaben kananan hukumomin Kaduna Hoto: @UbaSaniUs
Asali: Twitter

An sanar da sakamakon zaben jihar Kaduna

Shugabar KADSIECOM, Hajara Mohammed ta sanar da sakamakon awanni bayan an ce mutane su fito su kada kuri’arsu.

Kara karanta wannan

Kaduna: APC ta lallasa PDP da sauran jam'iyyun adawa a zaben ciyamomi

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Legit Hausa ta tattaro sunayen wadanda aka zaba a matsayin shugabannin kananan hukumomin 23 da ke jihar Kaduna.

Daily Trust ta ce APC ta yi wa sauran jam'iyyun adawa rugu-rugu a zaben ranar Asabar.

Za a samu sababbin ciyamomi a jihar Kaduna

Daga cikin fitattun wadanda aka zaba akwai Dauda Ilya Abba wanda kafin yanzu shi ne shugaban hukumar nan ta KADEDA.

Akwai Jamil Ahmad Muhammad wanda aka fi sani da JAGA, shi ne ya yi takara da tsohon ‘dan majalisa, Sulaiman I. Dabo.

Mace guda ce a cikinsu; Larai Sylvia Ishaku wanda za ta rike karamar hukumar Jaba.

Muhammad Jamilu Abubakar wanda aka fi sani da Albani Samaru ne zai zama shugaban karamar hukumar Sabon Gari.

Zababbun shugabannin kananan hukumomin Kaduna

1. Salisu Isah (Birnin Gwari)

2. Manzo Daniel Maigari (Kachia)

Kara karanta wannan

Kananan hukumom: Yan sanda sun tarwatsa matasa, an fadi halin da ake ciki a Kaduna

3. Rayyan Husseini (Kaduna ta Kudu)

4. Dr. Bashir Yanko Dawaki (Kauru)

5. Injiniya Jamil Ahmad Muhammad (Zariya)

6. Ahmad Sama’ila (Giwa)

7. Sani Abdul (Igabi)

8. Muhuyiddeen Abdullahi Umar (Kagarko)

9. Sankyai Obadiah Sanko (Kaura)

10. Muhammad Jamilu Abubakar (Sabon Gari)

11. Anton Usman (Sanga)

12. Jafaru Ahmed (Lere)

13. Garba Mohammad Sabon Gari (Makarfi)

14. Bashir Mamman Dogon Koli (Ikara)

15. Peter Tanko Dogara (Jema’a)

16. Injiniya Salasi Nuhu Musa (Chikun)

17. Joseph Bege Gaiya (Zangon-Kataf)

18. Dauda Iliya Abba (Kudan)

19. Muhammad Lawal Shehu (Soba)

20. Hon. Larai Sylvia Ishaku (Jaba)

21. Musa Saleh (Kubau)

22. Muhammad Gambo (Kaduna ta Arewa)

23. Dauda Madaki (Kajuru)

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng