Yan Bindiga Sun Watsa Taron Jam'iyya, Sun Sace Mataimakin Shugabanta na Kasa

Yan Bindiga Sun Watsa Taron Jam'iyya, Sun Sace Mataimakin Shugabanta na Kasa

  • An shiga tashin hankali bayan yan bindiga sun tarwatsa taron jam'iyyar LP a jihar Abia da ke Kudancin Najeriya
  • Maharan sun dauke jiga-jigan jam'iyyar ciki har da mataimakin shugaban LP ta kasa a yau Asabar 19 ga watan Oktoban 2024
  • Daga cikin wadanda aka sace akwai mukaddashin shugaban jam'iyyar a jihar, Prince G. O. Ndubueze yayin harin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Abia - Wasu yan bindiga sun yi garkuwa da jiga-jigan jam'iyyar LP a jihar Abia da ke Kudancin Najeriya.

Maharan sun boye fuskokinsu inda suka tarwatsa taron jam'iyyar da ake yi a birnin Aba da ke jihar.

Yan bindiga sun sace shugabannin jam'iyya ana tsaka da taro
Yan Bindiga sun tarwatsa taron jam'iyyar LP ana tsaka da taro. Hoto: Legit.
Asali: Original

Yan bindiga sun sace mataimakin shugaban LP

Kara karanta wannan

2027: Bayan hukuncin kotu, Jam'iyyar LP ta fadi ainihin wanda take yi wa aiki

Vanguard ta ruwaito cewa maharan sun sace mataimakin shugaban jam'iyyar ta kasa, Ceekay Igara.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Har ila yau, maharan sun yi garkuwa da mukaddashin shugaban jam'iyyar a jihar Abia, Prince G. O. Ndubueze yayin harin.

Maharan sun tabbatarwa jiga-jigan jam'iyyar cewa umarni ne daga sama inda suka gargade su kan turjiya.

Matasa sun barke da Zanga-zanga ta barke

Daily Post ta ce magoya bayan jam'iyyar akalla 500 ne suka fusata da lamarin inda suka durfafi babban ofishin yan sanda da ke birnin Aba.

Masu zanga-zangar sun nuna damuwa kan yadda ake neman kawo cikas ga cigaban dimukraɗiyya a jihar.

Wasu majiyoyi sun tabbatar da cewa ana zargin gwamnan jihar da hannu kan lamarin wanda ya kara ruruta rikicin jam'iyyar a jihar.

Yan bindiga sun hallaka babban dan sanda

Kun ji cewa wasu miyagun ƴan bindiga sun kai hari kan jami'an ƴan sanda da ke gudanar da aikin sintiri a garin Aba na jihar Abia.

Kara karanta wannan

Katsina: Yan bindiga sun sace shugaban jam'iyyar APC, sun kashe jami'in tsaro

Ƴan bindigan waɗanda suka buɗewa jami'an tsaron wuta inda suka hallaka wani Sufeton ƴan sanda tare da wasu mutum uku.

Jami'ar hulɗa da jama'a ta rundunar ƴan sandan jihar wacce ta tabbatar da aukuwar lamarin ta ce jami'an sun hallaka mutum biyu daga cikin ƴan bindigan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.