Kananan Hukumomi: Yan Sanda Sun Tarwatsa Matasa, An Fadi halin da Ake Ciki a Kaduna
- Yan sanda sun tarwatsa wasu matasa da ke kokarin kawo cikas a zabukan kananan hukumomi da ake cigaba da yi
- Jami'an tsaro sun jefa barkonon tsohuwa kan matasan da ke neman ta da rigima a ofishin hukumar zaben jihar da ke Gwantu
- Hakan ya biyo bayan cigaba da zaben kananan hukumomi a jihar Kaduna da ake yi a yau Asabar 19 ga watan Oktoban 2024
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kaduna - Yayin da ake cigaba da zaben kananan hukumomi a jihar Kaduna, an fara samun matsala.
Wasu matasa sun durfafi ofishin hukumar zaben jihar, KADSIECOM a yau Asabar 19 ga watan Oktoban 2024.
Yan sanda sun watsa matasa a Kaduna
Yan sanda sun tarwatsa matasan da ke faman tada rigima a ofishin hukumar zaben jihar, kamar yadda Aminiya ta wallafa bidiyo.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Lamarin ya faru ne a ofishin hukumar zaben jihar da ke garin Gwantu a jihar Kaduna da ke Arewa maso Yamma.
Rahotanni sun tabbatar da cewa an samu tsaiko a wurare da dama da ake gudanar da zabukan a yau Asabar 19 ga watan Oktoban 2024.
Mafi yawan wuraren da aka samu cikas ya faru ne saboda rashin zuwan jami'an hukumar a kan lokaci.
Karanta labarai game da zabukan kananan hukumomi
- Jigawa da Ribas: Yadda Aka Ci Yan Adawa da Yaki a Zaben Kananan Hukumomi
- APC Ta Tsorata, Ta Janye daga Fafatawa a Zaben Kananan Hukumomi, Ta Fadi Dalili
- Jerin Jihohin 3 Inda APC da PDP Za Su Fafata a Zaben Yau
Kananan hukumomi: Halin da ake ciki a Kaduna
Kun ji cewa Mutane a birnin Kaduna sun yi biris da dokar hana zirga-zirga da gwamnatin jihar ta sanya domin zaɓen ƙananan hukumomin jihar.
Masu ababen hawa sun ci gaba da gudanar da harkokinsu duk kuwa da dokar hana zirga-zirgar da aka sanya a ranar Asabar, 19 ga watan Oktoba 2024 .
Tun da farko dai gwamnatin jihar ta sanya dokar hana zirga-zirgar daga ƙarfe 6:00 na safe zuwa ƙarfe 7:00 na Yamma.
Asali: Legit.ng