Tsohon Gwamna a Arewa Ya Feɗe Gaskiya kan Rigimar Shugabancin PDP na Ƙasa
- Samuel Ortom ya bayyana cewa babu wani ɓangare a jam'iyyar PDP ta kasa kamar yadda ake yaɗawa a baya-bayan nan
- Tsohon gwamnan jihar Benuwai ya ce Umar Damagum ne sahihin shugaban PDP na riko, babu wani tsagi da ya ɓalle
- Wannan na zuwa ne a lokacin da rigimar cikin gida ke ƙara kamari a babbar jam'iyyar adawa bayan wani tsagi ya naɗa Yayari Mohammed
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Benue - Tsohon gwamnan jihar Benuwai, Samuel.Ortom ya ce babu wani ɓangare na daban a PDP saɓanin yadda ake yaɗawa cewa jam'iyyar ta dare gida biyu.
Ortom, ɗaya daga cikin gwamnonin biyar da suka kafa tawagar G5 a kakar zaɓen 2023 ya ce Umar Damagum ne kaɗai sahihin shugaban PDP na ƙasa.
A cewarsa, duk wani kwamitin gudanarwa watau NWC da ba Damagum ke jagoranta ba, ba shi da alaƙa da babbar jam'iyyar adawa, Vanguard ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ortom ya yabi NWC karƙashin Damagum
Tsohon gwamnan ya yi wannan furuci ne a lokacin da ya karɓi bakuncin sababbin ƴan kwamitin gudanarwa na jihar Benuwai a gidansa na Makurɗi.
Ya ƙara da cewa NWC karkashin Damagum ya yi iyakar bakin ƙakarinsa duk da rigingimin cikin gida da suka addabi jam'iyyar PDP.
Samuel Ortom ya ce maimakon a durkusar da shugabannin jam'iyyar, kamata ya yi a tallafa musu da yi musu addu’a, in ji Tribune Nigeria.
Da gaske PDP ta rabe gida biyu?
"Babu wani ɓangare a PDP, muna nan a layin da aka san mu na kokarin tabbatar da adalci, gaskia da daidaito, ban gusa daga nan ba, ni mai biyayya ne ga jam'iyya.
"Ba mu son shiga cikin tawagar ƴan tawaye saboda haka muna tare da Damagum, yana bakin koƙarinsa, mun san babu ma'asumi kowa na iya yin kuskure.
"Kamata ya yi a yabawa yan kwamitin NWC karkashin Damagum maimakon a zauna ana zaginsu, sun yi ƙoƙari duk da kalubalen rigimar cikin gida."
- Samuel Ortom.
Makinde ya yi magana kan takara a 2027
A wani rahoton kuma gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde ya yi magana kan jita- jitar neman shugabancin kasa a zaɓen 2027.
Makinde ya ce shi mutum ne cikakke da ke da hankali wanda zai iya magana kan abubuwan da suka shafe shi.
Asali: Legit.ng