Ana Ganin Gwamna da Manya a Arewa na Neman Yardar Jonathan kan Tsayawa Takara a 2027

Ana Ganin Gwamna da Manya a Arewa na Neman Yardar Jonathan kan Tsayawa Takara a 2027

  • Rahotanni sun tabbatar da cewa akwai wasu manya a Arewacin Najeriya da ke neman dawowar tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan
  • Wasu gungun yan siyasa masu ƙarfin fada a ji suna kokarin neman yardar Jonathan domin tsayawa takara a zaben 2027
  • Hakan bai rasa nasaba da neman kawo cikas ga Bola Tinubu da ke wa'adinsa na farko kan shugabancin Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Wasu manya a Arewacin Najeriya na kokarin dawo da tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan takara a 2027.

Ana zargin wasu masu fada a ji a yankin na bukatar Jonathan ya sake tsayawa takara a zaɓen 2027.

Kara karanta wannan

Sojoji sun gano gidan da yan bindiga ke boye makamai, an kama mata da miji

An fara kiran Jonathan ya sake tsayawa takara
Wasu yan Arewa sun sake kiran Goodluck Jonathan ya kuma tsayawa takara a zaɓen 2027. Hoto: Goodluck Ebele Jonathan.
Asali: Facebook

An sake kiran Jonathan kan tsayawa takarar 2027

Tribune ta gano cewa akwai masu neman kakabawa yan Najeriya Jonathan domin cika shekaru takwas kan mulki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rahotanni sun tabbatar da cewa masu jagorantar tafiyar sun hada da wani gwamna a Arewa maso Gabas da tsohon Janar a Arewa maso Yamma.

Hakan bai rasa nasaba da neman dakatar da Bola Tinubu a zaben 2027 da suke zargin na neman lalata kasar.

Wannan na zuwa ne yayin da ake zargin akwai wasu da ke neman tsayar da dan takara daga Kudu domin takawa Tinubu birki.

Jonathan: An fara neman hadin kan mutane

An tabbatar da cewa yanzu haka kungiyar na zagayawa da neman hadin kan Jonathan domin cimma abin da ake nema.

Wasu majiyoyi sun tabbatar da cewa masu wannan tafiya sun yi zama da masu irin tunaninsu a yankuna shida da suka hada da kungiyoyi da na kare hakkin dan Adam.

Kara karanta wannan

Tsohon gwamna ya bayyana babbar matsalar Najeriya da Tinubu ya fara magancewa

Jonathan ya caccaki bangaren shari'a a Najeriya

Kun ji cewa Tsohon shugaban ƙasa Goodluck Ebele Jonathan ya nuna damuwarsa kan wadu hukunce-hukuncen da ɓangaren shari'a ke yi.

Jonathan ya bayyana cewa wasu daga cikin hukunce-hukuncen da suka shafi al'amuran siyasa ko kaɗan babu adalci a cikinsu.

Ya nuna damuwarsa kan hukuncin da Kotun Ƙoli ta yanke wanda ya ba da dama mazaɓa ta dakatar da shugaban jam'iyya na ƙasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.