Ana cikin Rikicin NNPP a Kano, Jagororin Jam'iyyar Sun Koma APC
- Jam'iyyar NNPP ta sake samun koma baya a jihar Kano bayan wasu jagororinta sun sauya sheƙa zuwa APC mai adawa a Kano
- Jagororin jam'iyyar NNPP da suka sauya sheƙa zuwa APC sun fitp ne dagaa ƙananan hukumomin Tofa da Dawakin Tofa na Kano
- Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau Jibrin ya yi musu maraba zuwa APC a ofishinsa da ke Abuja
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Kano - Wasu jagororin jam'iyyar NNPP sun bar jar hula yayin da suka sauya sheƙa zuwa APC.
Jagororin na NNPP da suka sauya sheƙa zuwa APC sun fito ne daga ƙananan hukumomin Tofa da Dawakin Tofa na jihar Kano.
Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau Jibrin ya sanar da shigowarsu zuwa APC a shafinsa na X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jagororin NNPP sun koma APC a Kano
Sanata Barau ya bayyana cewa ƴan siyasan tare da ɗaruruwan magoya bayansu sun sanar da matakinsu na komawa APC a ofishinsa da ke majalisar dokokin tarayya Abuja.
Daga cikin sababbin mambobin akwai ɗan ajinsu Gwamna Abba Kabir Yusuf na Kano, Injiniya Isyaku Umar
Sanata Barau ya bayyana cewa waɗanda suka sauya sheƙa daga ƙaramar hukumar Dawakin Tofa sun samu jagorancin Alhaji Auwal Yusuf wanda ya sauya sheƙa daga jam’iyyar NNPP zuwa APC a ranar Alhamis.
Ya ƙara da cewa masu sauya sheƙar daga ƙaramar hukumar Tofa sun samu jagorancin Honorabul Yaro Inuwa Tofa, wanda bai daɗe da barin jam'iyyar NNPP ba.
"Sun yi zaɓi mai kyau ta hanyar yin wannan canjin sheƙa zuwa APC. APC jam'iyya ce ta kowa da kowa ba kamar NNPP ba."
- Sanata Barau I. Jibrin
Ƙusoshin NNPP sun koma APC
A wani labarin kuma, kun ji cewa Sanata Barau Jibrin ya sake sharewa jam'iyyar APC hanyar lashe zabe a jihar Kano da ya karbi kusoshin NNPP da suka sauya sheka.
A cikin ƴan watannin, ɗaruruwan jiga-jigan jam’iyyar NNPP ciki har da hadiman gwamnan Kano da magoya bayansa suka koma APC.
Asali: Legit.ng