Kano: Ana So a Raba Shi da Kwankwaso, Gwamna Abba Ya Amince da Ayyukan N36bn

Kano: Ana So a Raba Shi da Kwankwaso, Gwamna Abba Ya Amince da Ayyukan N36bn

  • A zaman da aka yi ranar Alhamis, 17 ga watan Oktoba 2024, gwamnatin jihar Kano ta yanke wasu muhimman hukunci
  • Majalisar zartarwa ta amince da wasu ayyuka da za su ci biliyoyin kudi domin inganta rayuwar mutanen jihar Kano
  • A karkashin jagorancin Abba Kabir Yusuf, an yi na'am da Naira biliyan 36.2 da za a kashe domin kwangiloli dabam-dabam

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Kano – A ranar Alhamis, 17 ga watan Oktoba 2024, gwamnatin Kano karkashin Abba Kabir Yusuf ta amince da jerin wasu ayyuka.

A zaman majalisar zartarwa da aka yi ne aka yanke hukuncin. Wannan ne karo na 19 da majalisar ta zauna bayan kafa gwamnati.

Gwamna Abba
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya amince da wasu ayyuka da za a yi a Kano Hoto: Abba Kabir Yusuf
Asali: Facebook

Abba: Majalisar SEC ta zauna a Kano

Kara karanta wannan

‘Yan APC da suka koma kuka da gwamnati saboda tsadar rayuwa a zamanin Tinubu

A Facebook Ibrahim Adam ya wallafa bayanan da aka samu daga ofishin sakataren gwamnatin Kano bayan zaman majalisar SEC.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Adam wanda hadimin Rabiu Kwankwaso ne, ya ce ayyukan da gwamnatin ta amince za ta yi a kauyukan Kano za su ci N28.3b.

Ayyukan da aka amince da su a jihar Kano

Kwamishinan labarai, Halliru Baba Dantiye, wanda aka dakatar daga NNPP a rikicin siyasa ya yi wa ‘yan jarida bayani na musamman.

Halliru Baba Dantiye ya ce daga cikin ayyukan da aka amince da su akwai kara kudin kwangilar gyaran asibitin nan na Abdullahi Wase.

Haka zalika an kara kudin aikin gyara cibiyar wasanni da ke Karfi a karamar hukumar Kura da kwangilar makarantar jinya a Madobi.

Sauran ayyukan da gwamna Abba zai yi

Gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta kuma karbe kwangilar hanya zuwa garin Madobi.

Kara karanta wannan

Kano: Muhimman abubuwa 5 game da kwamishinan da aka kama da zargin lalata da matar aure

Cikin ayyukan da aka sake duba kudinsu akwai titi da ya taso daga gidan gwamnati har zuwa otel din Daula, kwangilar za ta ci N674m.

A bangaren ilmi, makarantar Sa’adatu Rimi za ta ci fiye da N100m wajen aikin tantance kwas-kwas.

Sanarwar ta ce za a biya kudin kammala gina titin kilomita biyar da aka yi a Garko kuma za a gyara ofisoshi a gidan Murtala kan N700m.

Akwai ayyuka na musamman da za a yi a kananan hukumomi da za su ci kusan N2bn. A karshe komai ya tashi ne a kan fiye da N36bn.

Yaron Ganduje ya hadu da gwamnan Kano

Abdul'aziz Abdullahi Umar Ganduje ya hadu da gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf da ya je Abuja kamar yadda labari ya gabata kwanaki.

A baya an ga yaron na Ganduje tare da jagoran Kwankwasiyya da NNPP, Rabiu Musa Kwankwaso, ana tunanin zai iya shiga jam’iyyar NNPP.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng