'Ban Tsoron Komai': Gwamnan PDP Ya Magantu kan Kalubalantar Tinubu a 2027
- Yayin da ake hasashen yana neman shugabancin Najeriya, Gwamna Seyi Makinde ya yi martani kan haka
- Makinde ya bayyana haka ne yayin da ake jita-jitar yana neman kalubalantar Bola Tinubu a zaben 2027
- Makinde ya ce a yanzu ya yi girman da zai bayyana muradinsa idan yana so ba tare da tsoron kowa ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Oyo - Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde ya yi magana kan jita-jitar neman shugabancin kasa.
Makinde ya ce shi mutum ne cikakke da ke da hankali wanda zai iya magana kan abubuwan da suka shafe shi.
2027: Makinde ya magantu kan kalubalantar Tinubu
Gwamna Makinde ya bayyana haka ne kan zargin yana kokarin kalubalantar Bola Tinubu a zaben 2027, cewar Vanguard.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Makinde ya ce bai kamata ana juya masa magana ba musamman game da siyasar 2027 da cewa ya kai ya kare kansa.
"Ba mu yi ganawa ta PDP ba saboda wani na son shugabancin kasa ko wani abu ba."
"Abun da nake son cewa shi ne na yi girman da duk abin da nake so zan fito na fada ko mene."
"Domin haka babu wani maganar jita-jita, idan ina son neman wani mukami zan yi idan lokaci ya yi, babu mai tilasta ni."
- Seyi Makinde
Gwamna Makinde ya yabawa al'ummar jihar Oyo
Gwamna Makinde ya yabawa al'ummar Oyo kan goyon baya da suke cigaba da nuna masa tun farkon zuwansa mulkin jihar.
Ya ce a matsayinsa na gwamna ya yi nasarar cimma abubuwa da dama bayan samun kalubale daga magauta.
Gwamna ya fadi tasirinsa a zaben 2027
Kun ji cewa Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo ya shawarci masu neman kujerarsa da su kasance masu hakuri da juriya kan lamarin.
Makinde ya ce tabbas zai taka rawa wurin zaben wanda zai gaje shi inda ya ce hakan ba ya na nufin shi zai yi komai ba.
Gwamnan Oyo ya bukaci masu sha'awar gadon kujerarsa da su yi hakuri saboda sai lokacin zaben za su san matsayarsu.
Asali: Legit.ng