Jerin Jihohin 3 Inda APC da PDP Za Su Fafata a Zaben Yau
- Jam’iyyun siyasa na APC da PDP za su sake fafatawa a zaɓen ƙananan hukumomi a jihohin Kaduna da Kogi
- A Kaduna ƴan takara 79 ne za su fafata a zaɓen waɗanda suka fito daga jam’iyyun siyasa 10 da suka haɗa da APGA, APC, PDP, NNPP, PRP, LP, YPP, ADC, ZLP da AA
- Hakazalika, za a gudanar da zaɓen kansiloli a mazaɓu tara na ƙananan hukumomi shida na jihar Plateau
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Masu kaɗa kuri’a a jihohin Kaduna da Kogi za su fito a yau domin zaɓen sababbin shugabannin ƙananan hukumomi da kansiloli.
A jihar Kaduna, ƴan takara 79 za su fafata a zaɓen na ranar Asabar, 19 ga watan Oktoban 2024.
Daily Trust ta ce kwamishinan hulɗa da jama’a da yaɗa labarai na hukumar zaɓen jihar, Farfesa Joseph Gambo, ya bayyana cewa ƴan takarar sun fito ne daga jam'iyyu 10 da suka haɗa da APGA, APC, PDP, NNPP, PRP, LP, YPP, ADC, ZLP da AA.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sai dai kuma, ƴan adawa musamman na jam’iyyar PDP sun nuna damuwarsu dangane da yadda zaɓen zai gudana da kuma kalaman gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani.
Gwamnan wanda ɗan jam’iyyar APC ne, ya bayyana cewa jam’iyyarsa za ta lashe dukkanin kujerun, lamarin da ya sa aka fara tada jijiyoyin wuya.
PDP da wasu na zargin majalisar Kaduna kan zaɓe
Jam’iyyar PDP da sauran jam’iyyun adawa na iƙirarin cewa majalisar dokokin jihar Kaduna ta yi ƙoƙarin sauya dokokin zaɓe domin yin maguɗi, amma shugabannin APC sun musanta hakan.
Duk da tabbacin da hukumar zaɓen ta ba da, jam’iyyar PDP na ci gaba da taka-tsan-tsan, inda ta buƙaci a yi gaskiya da adalci.
Za a yi zaɓe a Kogi da Plateau
A jihar Kogi, an hana zirga-zirgar ababen hawa daga ƙarfe 7:00 na safe zuwa ƙarfe 4 na yamma domin samar da tsaro a zaɓen.
An buƙaci mutane da su fito su kaɗa ƙuri’a, yayin da aka samar da isasshen tsaro a rumfunan zaɓe.
Jihar Plateau na gudanar da zaɓen cike gurbi na kansiloli a mazaɓu tara na ƙananan hukumomi shida sakamakon wasu kura-kuran da aka samu a baya.
PDP ta lashe zaɓe a Plateau
A wani labarin kuma, kun ji cewa jam'iyyar PDP ta samu gagarumar nasara kan APC da sauran jam'iyyun adawa a zaben kananan hukumomin jihar Filato da aka gudanar Laraba.
Jam’iyyar PDP ta samu nasarar lashe kujerun kananan hukumomi 10 yayin da hukumar zaben Filato (PSIEC) ta fara bayyana sakamakon zaɓen.
Asali: Legit.ng