'Ko Yau za Mu Ci Zaɓe,' Sanatan APC ya Tono Dabarar Shawo Kan Talakawa

'Ko Yau za Mu Ci Zaɓe,' Sanatan APC ya Tono Dabarar Shawo Kan Talakawa

  • Sanata Orji Uzor Kalu ya yi magana kan yadda siyasar Najeriya za ta cigaba da gudana musamman a kan zaben shugaban kasa
  • Orji Uzor Kalu ya bayyana cewa ko yau aka saka zabe a Najeriya yana da tabbacin cewa jam'iyyar APC za ta lashe kuri'u
  • Sanatan bai nuna shakku ba a kan zabe duk da yadda ake fama da wahalar rayuwa a Najeriya a karkashin mulkin jam'iyyarsa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Sanata Orji Uzor Kalu ya bayyana cewa yan Najeriya za su zabi jam'iyyar APC yayin zabe.

Sanata Orji Uzor Kalu ya ce ba shi da kokonto a kan cewa idan suka nemi a zabe su yan Najeriya za su saurare su.

Kara karanta wannan

"Na cancanta," Sanatan APC ya bayyana shirinsa na neman zama shugaban ƙasa a 2027

Sanata Kalu
Sanata ya ce APC za ta ci zabe a Najeriya. Hoto: Senator Orji Uzor Kalu.
Asali: Facebook

Sanata Kalu ya bayyana haka ne a wata hira da ya yi da Channels Television kamar yadda talabijin din ya wallafa bidiyon a Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ko yau APC za ta ci zaɓe inji Kalu

Sanata Orji Uzor Kalu mai wakiltar Abia ta Arewa ya ce ba ya shakka a kan cewa APC za ta iya cin zabe a Najeriya.

Duk da wahalar rayuwa a Najeriya, Orji Uzor Kalu ya ce ko a yau aka ajiye akwatin zabe APC za ta yi nasara a kasar nan.

Dabarar da APC za ta yi yayin zabe

Sanata Orji Kalu ya bayyana cewa idan suka lallaɓi yan Najeriya ya san tabbas za su zabe su kuma in za a yi zabe a yau hakan za su yi.

Ya kara da cewa shi ya san zai cinye zabe a mazabarsa kuma dukkan yan APC za su kawo mazabunsu, daga nan kuma sun samu nasara.

Kara karanta wannan

'Yana yawo cikin dare,' Sanata ya tona yadda Tinubu yake zagaya gari a boye

Ya kuma kara da cewa a yanzu haka suna da dimbin magoya baya a Najeriya saboda haka cin zabe ba zai ba su wahala ba.

APC za ta ci zabe a Abia?

A yanzu haka dai dan jam'iyyar Labour, Alex Otti ne ke rike da kujerar gwamnan jihar Abia amma Sanata Kalu ya ce APC ce za ta kwace kujerar a zabe mai zuwa.

Kalu ya bayyana cewa ko gwamna Alex Otti ya dawo APC ko bai dawo ba za su samu nasara a zabe mai zuwa.

APC ta rabu gida 2 a Bayelsa

A wani labarin, Legit ta ruwaito cewa an samu rikicin siyasa a jihar Bayelsa inda shugabannin APC suka rabu gida biyu.

Shugabannin APC sun rabu gida biyu ne a kan korar ministan man fetur Sanata Heineken Lokpobiri daga jam'iyyar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng