"Na Cancanta," Sanatan APC Ya Bayyana Shirinsa Na Neman Zama Shugaban Ƙasa a 2027
- Sanata Orji Kalu ya bayyana cewa yana da gogewar zama shugaban kasa idan jam'iyyar APC ta ba shi dama a 2027
- Kalu, tsohon gwamnan jihar Abia ya ce a shirye yake ya nemi takara a 2027 idan Bola Tinubu ya haƙura da tazarce
- Kalu ya ce lissafinsa shi ne dawowa majalisar dattawa amma idan ya samu dama, zai nemi kujera lamba ɗaya a Najeriya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Tsohon gwamnan Abia kuma Sanata mai wakiltar Abia ta Arewa, Orji Uzor Kalu, ya bayyana cewa ya cancanci zama shugaban kasa a 2027.
Sanata Orji Kalu ya bayyana cewa zai nemi zama shugaban a 2027 idan har shugaba Bola Ahmed Tinubu bai nemi tazarce ba.
Orji Kalu ya yi wannan furucin ne ranar Alhamis a wata hira da gidan talabijin na Channels cikin shirinsu na siyasa a yau.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Zan iya mulkin Najeriya" - Sanata Kalu
"Bari na faɗa muku ni nan na cancanci zama shugaban Najeriya, ina da gogewa da kwarewar da ake bukata to amma muna da ɗan takara a jam'iyyarmu ta APC sai dai idan ya haƙura.
"Idan kuma jam'iyyarmu ta ba ni dama, ta miƙa mani tikitin takarar shugaban ƙasa, ta karrama ni, ba wani abu ba ne da zan tsaya tunani domin ba ni kaɗai ya shafa ba, dama ce na samu.
"Sai dai ni a lissafi na majalisar dattawa zan sake dawowa a 2027 na kara yi wa ƙasata hidima."
- Orji Uzor Kalu.
Abin da ya kawo matsi a Najeriya
Da yake tsokaci kan halin matsin da ƙasar nan ke ciki, tsohon gwamnan ya ce ba komai ya jawo haka ba sai rashin ingantaccen tsarin tattalin arziki.
Sanata Kalu na APC ya ce a ra'ayinsa, ya kamata gwamnati ta rage kashe-kashen kuɗi barkatai, kamar yadda Punch ta ruwaito.
Ya ce shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu na iya bakin ƙoƙarinsa wajen dawo da komai kan hanya amma ta yiwu a matsayinsa na ɗan adam ya yi kuskure a wani wurin.
Jigo ya nemi Kwankwaso, Atiku su taimaka
A wani rahoton kuma tsohon kwamishina a Kano ya bayyana irin gudummuwar da ake bukata daga Rabiu Kwankwaso, Atiku Abubakar da Peter Obi.
Musa Iliyasu Kwankwaso ya ce lokaci ya yi da manyan ƴan siyasar za su jingine adawa, su taimaki ƴan Najeriya a halin da ake ciki.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng