Barau Ya Sake Sharewa APC Hanyar Lashe Zabe a Kano, Kusoshin NNPP Sun Sauya Sheka
- Jam'iyyar NNPP ta sake gamuwa da matsala a jihar Kano da wasu kusoshinta suka sauya sheka zuwa APC mai mulki a kasa
- Sanata Barau Jibrin wanda ya karbi jiga-jigan da suka sauya shekar ya ce sun shaida masa cewa sun gamsu da tsare-tsaren APC
- Mataimakin shugaban majalisar dattawan ya yi wa wadanda suka sauya shekar alkawarin kula da su kamar sauran 'yan jam'iyyar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Sanata Barau Jibrin ya sake sharewa jam'iyyar APC hanyar lashe zabe a jihar Kano da ya karbi kusoshin NNPP da suka sauya sheka.
A cikin 'yan watannin, daruruwan jiga-jigan jam’iyyar NNPP ciki har da hadiman gwamnan Kano da magoya bayansa suka koma APC.
Kusoshin NNPP sun koma APC a Kano
Mataimakin shugaban majalisar dattawan ya wallafa a shafinsa na X a safiyar ranar Juma'a cewa:
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"A jiya ne na karbi bakuncin Alhaji Auwalu Yusuf Dawakin Tofa da sauran 'yan jam'iyyar NNPP da suka sauya sheka zuwa APC.
"Sun nuna cewa gamsuwa da yadda mu ke tafiyar da harkokin siyasa da kuma nasarorin da muka samu a fadin jiharmu, sun kuma koka da irin rikon da aka yi masu a NNPP."
- Sanata Barau I. Jibrin
A tarurruka daban-daban a majalisar tarayya, jiga jigan na NNPP suka bayyana ficewa daga jam’iyyarsu zuwa APC ta hannun Sanata Barau.
Barau ya yi maraba da tsofaffin 'yan NNPP
Sanata Barau ya ba su tabbacin cewa APC ta na da girman da za ta dauki kowa kuma za a yi musu adalci da mutuntawa kamar sauran ‘yan jam'iyyar.
"Jam’iyyarmu ta APC ita ce babbar jam’iyyar siyasa a Afirka. Ba kamar jam’iyyar NNPP da mutum daya tilo ke jan linzaminta ba, APC na da tsarin jagoranci."
- A cewar Barau I. Jibrin
Mataimakin shugaban majalisar ya ce babu zagi ko yarfe a tsarin siyasarsu yana mai cewa ci gaban talakawa da bunkasa rayuwarsu ce suka saka a gaba.
An soki Barau kan karbar 'yan adawa
A wani labarin, mun ruwaito cewa wata ma’abociyar dandalin sada zumunta na X ta fusata da yadda ta ce Barau Jibrin ya fi mayar da hankali kan siyasa.
Adda Fadi ta nuna mamakin yadda mataimakin shugaban majalisar ya yi biris da matsin rayuwa da rashin tsaron da Arewa ke ciki, 'sai karban mutane.'
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng