Ana Tsaka da Rikicin PDP, Jam'iyyar APC Ta Fadi Alakar da Ke Tsakaninta da Wike
- Jam’iyyar APC mai mulki a kasa ta yi karin haske kan alakar da ke tsakaninta da ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike
- A wata hira da aka yi da shi, shugaban APC na Ribas, Tony Okocha, ya ce Wike mai kishin PDP ne kuma ba zai taba sauya sheka ba
- Da yake magana kan rikicin Ribas, Okocha ya kara bayyana cewa Wike da ‘yan majalisa 27 a jihar ba ‘ya’yan jam’iyyar APC ba ne
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Ribas - Shugaban APC a Ribas, Dakta Tony Okocha, ya bayyana cewa ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike ba dan jam’iyyarsu ba ne.
A cewarsa, Nyesom Wike ba zai taba barin jam’iyyar adawa ba, yana mai cewa, “ya dade yana cewa PDP ta yi masa gata, ba zai bar ta ba."
"Wike ba zai bar Jam'iyyar PDP ba" - APC
Jaridar Punch ta rahoto Tony ya jaddada maganarsa ta cewa ministan babban birnin tarayya ba zai taba fita daga jam'iyyar PDP ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Wike ba zai taba barin PDP ba. Shi mai kishin PDP ne. Ba zai iya barin wannan jam'iyyar ba.
“Ya kasance yana cewa PDP ce ta mayar da shi yadda yake yanzu. Kullum yana cewa zai ci gaba da kasancewa a jam'iyyar, ba zai barta ba.""
- Shugaban APC, Tony Okoccha
Alakar da ke tsakanin Wike da APC
Dakta Tony ya bayyana cewa ‘yan majalisar Ribas 27, wadanda a halin yanzu ke takun sakar siyasa da Gwamna Siminalayi Fubara, su ma ba ‘ya’yan jam’iyyar APC ba ne.
“Mutane sun ce Wike ya koma APC. Kazalika sun ce ‘yan majalisa 27 da ke fada da Fubara a halin yanzu suma sun koma APC.
"Bari na fayyace maku gaskiyar lamari. Duk da cewa ina fatan samun su a cikin jam'iyyata, amma a yanzu babu wanda ya yarda ya shigo tafiyarmu.
“Idan za su canja sheka, dole ne su je gundumominsu, su yi rajista, kuma su karbi katin zama 'yan jam'iyya. Babu wanda ya yi hakan a cikinsu."
- Tony Okocha
Wike ya hadu da shugaban jam'iyyar APC
A wani labarin, mun ruwaito cewa Nyesom Wike ya kai ziyara gidan shugaban jam’iyyar APC na kasa, Abdullahi Umar Ganduje, suka yi doguwar tattaunawa.
Wannan na zuwa yayin da ake rade radin cewa Nyesom Wike, wanda ya yi wa jam’iyyar APC aiki a zaben shugaban kasa na 2023, ya na shirin sauya-sheka.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng