‘Alamar Matsala tsakanin Tinubu da Shettima,’ Hadimin Osinbajo Ya Fito da Bayanai

‘Alamar Matsala tsakanin Tinubu da Shettima,’ Hadimin Osinbajo Ya Fito da Bayanai

  • Rashin shugaban kasa da kuma mataimakinsa a Najeriya a lokaci daya na cigaba da daukan hankalin masana da talakawa
  • Tsohon hadimi a fadar Aso Rock, Laolu Akande ya ce sam bai dace a ce shugaban kasa da mataimakinsa sun yi tafiya ba
  • Akande ya bayyana cewa wannan shi ne karo na biyu da aka samu haka a mulkin Bola Tinubu kuma zai iya haifar da matsala

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Yan Najeriya na cigaba da tofa albarkacin bakinsu kan rashin samun shugaban kasa da mataimakinsa a lokaci daya.

Tsohon hadimin mataimakin shugaban kasa, Loalu Akande ya ce babu dacewa a ce an rasa duka shugabannin Najeriyan a cikin kasa.

Kara karanta wannan

Tsohon gwamna ya bayyana babbar matsalar Najeriya da Tinubu ya fara magancewa

Tinubu
Hadimin Osinbajo ya yi magana kan tafiyar Tinubu da Shettima. Hoto: Kashim Shettima
Asali: Facebook

Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa Akande ya ce an taba samun irin haka sau daya a mulkin shugaba Muhammadu Buhari.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Akande ya soki tafiyar Tinubu da Shettima

Tsohon hadimin mataimakin shugaban kasa, Laolu Akande ya ce tafiyar Bola Tinubu da Kashim Shettima kasashen waje a lokaci daya zai iya haifar da matsala.

Rahoton Channels Television ya nuna cewa Louku Akande ya ce ya kamata duk halin da za a shiga a samu daya daga cikinsu yana gida Najeriya.

Akande ya kara da cewa idan ana samun irin haka ba lallai amana da ke tsakaninsu ta cigaba da wanzuwa ba.

Ga abin da yake cewa:

Bai kamata a ce shugaban kasa da mataimakinsa su fita a Najeriya ba a lokaci daya.
Hakan sam bai dace ba, kuma alama ce da ke nuna cewa za a iya samun matsalar amana a tsakanin shugaban kasa da mataimakinsa idan aka ɗauki lokaci ana haka.

Kara karanta wannan

"A rage ciki:" Ministan Tinubu ya ce babu kudi a kasa, ya aikawa magidanta shawara

- Laolu Akande, tsohon hadimin Osinbajo

Akande ya bayyana cewa sau daya aka samu Buhari da Yemi Osinbajo sun fita daga Najeriya a lokacin ɗaya da suke mulki.

Shettima ya isa kasar Sweden

A wani rahoton, mun ruwaito muku cewa mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya isa Sweden domin wata muhimmiyar tattaunawa.

Sanata Kashim Shettima ya samu rakiyar gwamnan jihar Filato da wasu manyan jami'an gwamnati yayin ziyarar da za su yi zuwa kasar Turan.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng