Amaechi Ya Fadi Rikicinsa da Tsohon Gwamnan APC har Ya Kai Shi Kara Wurin Buhari

Amaechi Ya Fadi Rikicinsa da Tsohon Gwamnan APC har Ya Kai Shi Kara Wurin Buhari

  • Tsohon gwamnan Rivers, Rotimi Amaechi ya fadi yadda suka kusa kaurewa da tsohon gwamna Akinwumi Ambode
  • Tsohon Ministan sufuri a lokacin mulkin Muhammadu Buhari ya ce sabanin ya faru ne saboda ayyukan jiragen kasa
  • Amaechi ya ce Ambode ya ba shi ciwon kai, wanda har kararsa wurin Buhari da mataimakinsa, Yemi Osinbajo ya kai

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Lagos - Tsohon Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi ya fadi yadda suka samu matsala da tsohon gwamnan Lagos, Akinwumi Ambode.

Amaechi ya ce sun samu matsala da Ambode ne kan aikin tashar jiragen kasa s jihar Lagos.

Amaechi ya fadi yadda suka babe da tsohon gwamnan APC
Tsohon Minista, Rotimi Amaechi ya fadi yadda suka samu matsala da tsohon gwamnan Lagos. Hoto: Rotimi Chibuike Amaechi.
Asali: Facebook

Rotimi Amaechi ya kai karar Ambode wurin Buhari

Kara karanta wannan

Tsohon gwamna ya bayyana babbar matsalar Najeriya da Tinubu ya fara magancewa

Tsohon Ministan ya fadi haka ne a Lagos yayin wani taro da kungiyar TCAN ta shirya a yau Alhamis 17 ga watan Oktoban 2024, cewar Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Amaechi ya ce sai da ya kai karar Ambode wurin mataimakin shugaban kasa a wancan lokaci, Farfesa Yemi Osinbajo.

Ya ce abin ya girma wanda ya tilasta shi zuwa wurin Muhammadu Buhari domin shawo kan lamarin.

Yadda Amaechi ya babe da tsohon gwamna Ambode

Tsohon gwamnan Rivers ya ce a lokacin Ambode bai dauki lamarin da muhimmanci ba, shi ne dalilin samun matsalarsu.

"An yi ayyukan jiragen kasa a jihar Rivers amma gaskiya Lagos ta yi kokari sosai a wannan fanni."
"Wannan shi ne wurin da na kusa samun matsala da tsohon gwamnan Lagos, Akinwumi Ambode saboda ya fara gajiya da lamarin."
"Na yi kokarin shawo kansa, na fadawa Osinbajo har wurin Buhari na kai korafinsa kafin zuwan sabon gwamna."

Kara karanta wannan

An fayyace wanda ke rike da Najeriya bayan ficewar Tinubu da Kashim daga kasar

- Rotimi Amaechi

Amaechi ya bayyana muhimmancin jiragen kasa musamman a wannan yanayi da ake ciki na tsadar rayuwa.

Amaechi ya koka da zanga-zangar matasa

A wani labarin, kun ji cewa tsohon Ministan sufuri, Rotimi Amaechi ya yi magana kan zanga-zangar matasa da aka yi.

Amaechi ya ce bai taba tsammanin iya abin da matasan za su yi ba kenan saboda irin kunci da yan kasar suke ciki.

Wannan na zuwa ne yayin da matasa suka cika tituna a ranakun 1 zuwa 10 ga watan Agustan 2024 da ta gabata.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.