Yunkurin Tsige Ganduje daga Shugaban APC Ya Samu Cikas, Kungiyar Arewa Ta Ja baya

Yunkurin Tsige Ganduje daga Shugaban APC Ya Samu Cikas, Kungiyar Arewa Ta Ja baya

  • Kungiyar APC ta Arewa ta tsakiya ta dakatar da fafutukar da take yi na tsige Abdullahi Ganduje a matsayin shugaban APC
  • A 'yan watannin da suka gabata, Ganduje ya tsallake komar masu adawa da shugabancinsa musamman daga Arewa ta tsakiya
  • Kungiyar ta amince ta janye fafutukarta na tsige shugaban har zuwa lokacin da kwamitin zartarwar jam'iyyar zai yi taronsa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Fafutukar da mutane da wasu kungiyoyi ke yi na ganin an tsige Abdullahi Umar Ganduje daga shugaban APC na kasa ta gamu da cikas.

Wata gamayyar kungiyoyin APC daga Arewa ta tsakiya sun dakatar da fafutukar da suke yi na tsige Ganduje daga kujerarsa tare da bayyana dalili.

Kara karanta wannan

Ana 'lallaɓan' Tinubu ya saki ƙasurgumin ɗan ta'adda, bayanai sun fito

Kungiya a Arewa ta yi magana kan yunkurin tsige Ganduje daga shugaban APC
Kungiya daga Arewa ta dakatar da fafutukar tsige Ganduje daga shugaban APC. Hoto: @OfficialAPCNg
Asali: Twitter

Shugaban gamayyar kungiyoyin, Hon Abdullahi Sale Zazzaga ne ya bayyana hakan yayin wata tattaunawa da DCL Hausa a ranar Laraba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kungiya ta dakatar da adawa da Ganduje

Hon Abdullahi Sale Zazzaga ya ce gamayyar kungiyoyin za su tsahirta daga fafutukar saboda taron kwamitin zartarwar jam'iyyar da ke tafe.

Ya ce manyan jami’an yankin Arewa ta tsakiya sun gargadi gamayyar kungiyoyin da su guji tada zaune tsaye kan shugabancin APC.

Abdullahi Zazzaga ya ce tun farko sun fara fafutukarsu ne saboda kyautata siyasa da tattalin arzikin yankin, inji rahoton Daily Trust.

'Mun bi shawarar manya' - Kungiyar APC

Shugaban gamayyar kungiyoyin ya ce:

“Mun fito mun nuna adawarmu da kasancewarsa shugaban jam'iyya kuma an ji mu da babbar murya. Wannan ba shi ne karshen fafutukarmu ba. Muna yi ne domin al'umma.

Kara karanta wannan

Za a sasanta, kungiyar APC ta zubar da makamanta kan neman tsige Ganduje

“Mun dakatar da wannan adawar ne saboda mun tattauna da manyan mu. Muka zauna a teburin sasanci da su. Sun yi mana bayani game da taron NEC da ke tafe.
Sun bukaci mu bai wa kwamitin zartarwar damar yanke hukunci na karshe a kan lamarin. Kowa a kasar nan ya san mun yi adawa mai zafi saboda al’ummarmu da yankinmu."

APC: Kotu ta ki tsige Ganduje

A wani labarin, mun ruwaito cewa wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta ce ba za ta iya tsige Abdullahi Ganduje daga shugabancin APC na kasa ba.

Mai shari'a Inyang Ekwo ya ce nada shugabannin APC wani al'amari ne na harkokin jam'iyyar wanda babu wata kotu da za ta iya tsoma baki a ciki.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.