Masu Zanga Zangar Ganin An Tsige Ganduje a APC Sun Gamu da Babbar Matsala a Abuja

Masu Zanga Zangar Ganin An Tsige Ganduje a APC Sun Gamu da Babbar Matsala a Abuja

  • Ƴan daba sun huce fushinsu a kan masu zanga-zanga da ke son ganin an tsige Abdullahi Umar Ganduje daga shugabancin jam'iyyar APC
  • Ƴan daban sun farmaki masu zanga-zangar a birnin tarayya Abuja lokacin da suka nufi sakatariyar jam'iyyar ta ƙasa
  • Shugaban masu zanga-zangar a bayyana farmakin a matsayin abin kunya inda ya yi kira ga masu ruwa da tsaki na APC da su tabbatar Ganduje ya rasa kujerarsa

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Masu zanga-zangar ganin an tsige Abdullahi Umar Ganduje daga shugabancin jam'iyyar APC sun gamu da cikas a ranar Alhamis.

Wasu ƴan daba dai sun lakaɗawa masu zanga-zangar duka bayan sun je sakatariyar jam'iyyar APC suna neman a tsige Ganduje daga muƙaminsa.

Kara karanta wannan

Ganduje ya bayyana abubuwan da ke yi wa mata barazana a siyasar Najeriya

'Yan daba sun doki masu son a tsige Ganduje a APC
Masu zanga-zangar neman a tsige Ganduje sun sha duka a Abuja Hoto: @officialAPCNg
Asali: Twitter

'Yan 'a tsige Ganduje' sun samu cikas

Jaridar Punch ta ce ƴan daban ɗauke da sanduna sun farmaki masu zanga-zangar ne waɗanda suka fito daga otal ɗin Valential da ke Wuse 2, Abuja, lokacin da suke kan hanyar zuwa sakatariyar jam’iyyar APC ta ƙasa da ke kan titin Blantyre.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ƴan daban sun kuma ƙwace fastoci da tutocin masu zanga-zangar tare da lakaɗawa wasu daga cikin su dukan tsiya, cewar rahoton jaridar Daily Trust.

Masu zanga-zangar waɗanda suka ranta ana kare domin tsira da rayukansu sun haɗu a wani wuri a Wuse 2, inda shugabansu, Hamisu Suleiman Sardauna, ya yi magana a madadinsu.

Wane kira masu-zangar suka yi?

Hamisu Suleiman ya yi kira ga masu ruwa da tsaki a jam’iyyar da su tsige Ganduje tare da tabbatar da cewa an mayar da kujerar yankin Arewa ta tsakiya.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun yi awon gaba da jariri tare da mahaifiyarsa a jihar Kaduna

"Mu masu son zaman lafiya ne. Mu ƴan jam’iyya ne domin haka babu wanda ya isa ya hana mu adalci. Mun zo nan ne domin zanga-zangar lumana amma wasu ƴan daba sun lakaɗawa mambobinmu duka. Wannan abin kunya ne."
"Muna fafutukar ganin an yi adalci. Dole ne masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC su mayar da ofishin shugaban jam'iyyar na ƙasa zuwa yankin Arewa ta tsakiya."

- Hamisu Suleiman Sardauna

Shirin tsige Ganduje daga kujerar APC

A wani labarin kuma, kun ji cewa wani jigon APC a jihar Kogi, Atiku Abubakar Isah, ya bayyana cewa bai kamata a maye gurbin Abdullahi Ganduje a matsayin shugaban jam'iyyar na ƙasa ba.

Atiku ya ce Ganduje yana da gogewar da ake buƙata wajen jan ragamar jam'iyyar APC mai mulki saboda haka babu dalilin da zai sa a canza shi a halin yanzu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel