APC Ta Tsorata, Ta Janye daga Fafatawa a Zaben Kananan Hukumomi, Ta Fadi Dalili

APC Ta Tsorata, Ta Janye daga Fafatawa a Zaben Kananan Hukumomi, Ta Fadi Dalili

  • Yayin da ake shirin karasa zaben kananan hukumomi a jihar Plateau, APC ta bayyana matsayarta kan takarar
  • Jam'iyyar APC a jihar Plateau ta sanar da janyewarta daga zaben da za a yi a ranar 19 ga watan Oktoban 2024
  • Hakan ya biyo bayan ayyana zaben wasu unguwanni da ba a kammala ba saboda matsalolin da aka samu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Plateau - Jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya ta janye daga fafatawa a zaben kananan hukumomi.

Jam'iyyar a jihar Plateau ta ce ba za ta shiga zaben da za a kammala na kananan hukumomi ba.

APC ta janye a zaben kananan hukumomi da za a yi
APC ta janye a zaben kananan hukumomi da za a yi a jihar Plateau. Hoto: All Progressives Congress, People's Democratic Party, PDP.
Asali: Facebook

Plateau: APC ta ba magoya bayanta shawara

Kara karanta wannan

Zaben 2027: NNPP ta zargi APC da rura wutar rikici a sauran jam'iyyu

Leadership ta ce jam'iyyar ta bukaci magoya bayanta gaba daya a jihar su kauracewa zaɓen.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jam'iyyar na zargin hukumar zaben jihar ta PLASIEC da rashin mutunta dimukraɗiyya da zabin al'umma.

Sakataren yada labaran jam'iyyar a jihar, Shittu Bamaiyi ya ce babu dalilin shigar APC zaben da babu inganci, cewar Vanguard.

"Abin takaici ne kuma da dariya hukumar zaben jihar Plateau ta PLASIEC za ta ayyana zaben a matsayin wanda aka gudanar cikin adalci."
"Maganar gaskiya ya fi kamata a ce an rusa zaben ne saboda wasu korafe-korafe da jam'iyyun adawa suka kawo game da wasu matsaloli."

- Shittu Bamaiyi

PLASIEC ta yi magana kan sake zabe

Wannan na zuwa ne bayan ayyana zaben kananan hukumomi a wasu gundumomi da cewa ba su kammala ba saboda matsaloli.

Hukumar zaben jihar ta tabbatar da cewa akwai unguwanni 21 da ba a kansilolinsu satifiket ba saboda rashin kammala zaɓen.

Kara karanta wannan

Igbo sun yi nasarar lashe kujeru a zaben kananan hukumomi a Arewacin Najeriya

Igbo sun samu nasarar lashe kujeru a Plateau

Mun ba ku labarin cewa wasu yan kabilar Igbo sun yi nasarar lashe kujerun kansiloli a jihar Plateau da ke Arewacin Najeriya.

Hukumar zaben jihar, PLASIEC ita ta sanar da sakamakon zaben da aka gudanar na kananan hukumomi da kansiloli.

Hon. Austin Wachukwu ya yi nasarar zama kansilan unguwar Vanderpuye sai kuma Hon. Okoro Uzoma ya yi ci zaɓen unguwar Tafawa Balewa a Jos ta Arewa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.