Tazarcen Tinubu: Yadda Rikicin Jam’iyyun PDP, LP da NNPP zai iya ba APC Nasara a 2027

Tazarcen Tinubu: Yadda Rikicin Jam’iyyun PDP, LP da NNPP zai iya ba APC Nasara a 2027

  • Masana sun fara bahasi kan yadda lamarin siyasar Najeriya ke gudana a halin yanzu da abin da zai iya faruwa a gaba
  • Hakan na zuwa ne bayan an yawaita samun rikicin cikin gida a tsakanin manyan jam'iyyun adawa a Najeriya a wannan lokaci
  • An nuna yadda rikicin cikin gida a manyan jam'iyyun adawa zai iya shafar zaben shugaban kasa mai zuwa na shekarar 2027

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Yan siyasa sun fara hangen yadda zaben shugaban kasa zai gudana a Najeriya a shekarar 2027.

Masu fashin baki sun bayyana cewa rikicin jam'iyyun adawa zai iya ba APC nasara cikin sauki a 2027.

Kara karanta wannan

Rikicin jam'iyya: An bayyana lokacin da Damagum zai sauka daga shugaban PDP

Bola Tinubu
Yadda rikicin yan adawa zai shafi zabe. Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.
Asali: Twitter

Jaridar the Guardian ta yi rahoto kan yadda yan adawa suka gaza hada kai da magance matsalolinsu a Najeriya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rikicin jam'iyyun adawa a Najeriya

Manyan jam'iyyun adawa irinsu PDP, LP da NNPP duk suna fama da rikicin cikin gida musamman kan shugabanci.

Ana kallon har yanzu ba su gama daidaita cikin gidajensu ba balle a dawo maganar haɗaka domin tunkarar zaben 2027.

Yadda rikicin jam'iyyu ke tasiri a zabe

Shugaban kwamitin amintattun NNPP, Boniface Aniebonam ya ce a halin yanzu manyan yan adawa ba su da wani karfi saboda rikicin da ya mamaye su ta ɓangarori da dama.

Saboda haka ya ce jam'iyun adawa ba za su iya tabuka komai ba wajen kawo canji idan aka lura da halin da suke ciki a yau.

Sai dai duk da haka shugaban kwamitin amintattun APGA ya yi hasashen cewa yan adawa za su hada kai kafin a fara maganar zaben 2027 gadan gadan.

Kara karanta wannan

Karshensu Turji ya zo: Najeriya za ta shigo da jiragen yaki sama da 30

Maganar tazarcen Tinubu a 2027

Shugaban SDP, Olu Agunloye ya ce matuƙar yan adawa suna son samun nasara a zaben 2027 dole sai sun hada kai kafin tunkarar APC.

Ana ganin idan suka cigaba da rikici, shugaba Bola Ahmed Tinubu zai samu sauƙin musu ƙafa, ya wuce mulki karo na biyu a 2027.

An bukaci Kwankwaso ya ja da baya a NNPP

Legit ta ruwaito cewa tsagin jam'iyyar NNPP ya yi Allah wadai kan yadda Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ke nuna kansa a matsayin jagoran jam'iyyar.

Tsagin ya ce akwai bukatar a ladabtar da Abba Kabir Yusuf kan yadda yake cikakkiyar biyayya ga Rabi'u Kwankwaso a kan shugabancin NNPP.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng