Dan Takarar PDP da Shugaban Jam'iyya Sun Koma APC Ana Dab da Zabe

Dan Takarar PDP da Shugaban Jam'iyya Sun Koma APC Ana Dab da Zabe

  • Jam'iyyar APC ta samu ci gaba a jihar Kaduna yayin da ya rage sauran ƴan kwanaki a gudanar da zaɓen ciyamomi
  • Tsohon shugaban jam'iyyar LP na jihar Kaduna, Isah Chiroma tare da ɗan takarar kansila na PDP sun sauya sheƙa zuwa APC
  • Sun nuna gamsuwarsu kan yadda APC take gudanar da mulki, suka ce sun koma jam'iyyar ne domin a ciyar da jihar gaba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kaduna - Yayin da ya rage saura kwanaki uku a gudanar da zaɓen ƙananan hukumomi a Kaduna, tsohon shugaban jam’iyyar LP na jihar, Isah Chiroma, ya koma jam'iyyar APC.

Tsohon shugaban na LP ya sauya sheƙa ne zuwa APC tare da ɗan takarar kansila na jam’iyyar PDP a mazaɓar Kafanchan B, Abdullahi Imrah.

Kara karanta wannan

Karshen APC ya zo, PDP ta gama shirin karɓe kujerar wani gwamna a Najeriya

Dan takarar PDP ya koma APC a Kaduna
Tsohon shugaban LP ya koma APC a Kaduna Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Tsohon shugaban na LP a jihar ya koma APC ne a lokacin miƙa tutar jam'iyyar ga ƴan takararta a zaɓen da ke tafe, cewar rahoton jaridar Tribune.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Meyasa suka koma jam'iyyar APC?

Isah Chiroma ya bayyana cewa salon mulkin Sanata Uba Sani da kuma ci gaban da aka samu a Kudancin Kaduna ne ya sa ya yanke shawarar dawowa APC domin ciyar da jihar gaba.

The Guardian ta ce a na sa jawabin, Abdullahi Imrah ya ce duk da cewa ƴan kwanaki ne suka rage a yi zaɓen, ya yanke shawarar ficewa daga PDP.]

'Dan siyasar ya haɗe da Hon. Peter Tanko a jam’iyyar APC domin su haɗa kai wajen ciyar da jihar gaba.

An yi masu maraba zuwa jam'iyyar APC

Da take karɓar masu sauya sheƙar, mataimakiyar gwamnan Kaduna, Dakta Hadiza Sabuwa Balarabe, ta taya su murna da suka yanke shawarar shigowa APC.

Kara karanta wannan

Ana batun warware rikicin PDP, 'yan daba sun farmaki sakatariyar jam'iyyar

Mataimakiyar gwamnan ta ba su tabbacin cewa za a riƙa damawa da su ba tare da nuna musu bambanci ba.

APC ta dakatar da tsohon mataimakin gwamna

A wani labarin kuma, kun ji cewa APC reshen Bayelsa, ta dakatar da wani tsohon mataimakin gwamnan jihar, Werinipre Seibarugu da wasu har sai baba ta gani.

Jam'iyyyar APC ta dakatar da mutanen ne a reshenta na ƙaramar hukumar Yenagoa ta jihar bisa zargin yi wa jam'iyyar zagon ƙasa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng