Babban Jigo a Kano Ya Zuga Gwamna Abba, Ya Soki Tsarin Rabiu Kwankwaso

Babban Jigo a Kano Ya Zuga Gwamna Abba, Ya Soki Tsarin Rabiu Kwankwaso

  • Tsohon kwamishina a Kano, Musa Iliyasu Kwankwaso ya caccaki jagoron Kwankwasiyya kan rikicin da ya ɓarke a NNPP
  • Babban jigon na APC ya ce Kwankwaso ne ya kitsa dakatar da sakataren gwamnatin Kano saboda cimma burinsa na siyasa
  • Musa Iliyasu ya ce abin da ke faruwa a NNPP ya tabbatar da abin da yake yawan faɗa kan taurin kai da kwaɗayin mulkin Kwankwaso

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kano - Fitaccen ɗan siyasar nan a Kano kuma jigon APC, Musa Iliyasu Kwankwaso ya caccaki jagoran NNPP na ƙasa, Sanata Rabiu Kwankwaso.

Musa Iliyasu ya soki Kwankwaso ne kan dakatarwan da aka yi wa sakataren gwamnatin jihar Kano, Abdullahi Baffa Bichi daga NNPP.

Kara karanta wannan

Kwankwaso ya share hanyar 2027 ga Abba, ya yi wa siyasar APC illa

Rabiu Kwankwaso.
Musa Iliyasu Kwankwaso ya caccaki jagoran NNPP kan dakatar da sakataren gwamnatin Kano Hoto: Rabiu Musa Kwankwaso
Asali: Facebook

Jigon na APC ya ce dakatar da Baffa Bichi daga NNPP ya ƙara tabbatar da abin da ya daɗe yana nanatawa kan taurin kan Kwankwaso a siyasa, kamar yadda Tribune Nigeria ta kawo.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dakatar da Bichi: Jigon APC ya caccaki Kwankwaso

Musa Iliyasu ya bayyana Kwankwaso a matsayin ɗan siyasar da ba ya ganin kowa da gemu kuma zai iya taka kowa don cimma burinsa.

"Dakatar da sakataren gwamnatin Kano ya tabbatar da abin da nake yawan faɗa kan Kwankwaso. Ya nuna zai iya take duk wanda ya shiga hanyarsa," in ji shi.

Musa Iliyasu ya kuma ƙaryata ikirarin Kwankwaso cewa shugaban NNPP na Kano, Hon. Hashim Dungurawa ne kaɗai ke da alhakin dakatar da SSG.

'Kwankwaso ne ya kitsa dakatar da Bichi'

A cewarsa, jagoran ƴan Kwankwasiyya ne ya kitsa dakatar da Bichi saboda yana son nuna ƙarfin ikonsa kan Gwamna Abba Kabir Yusuf.

Kara karanta wannan

Rikicin NNPP: Gwamna Abba ya juyawa Kwankwaso baya kan mutum 2 a Kano

“Na sha fada cewa burin Kwankwaso ya rika juya gwamna ta ko ina domin cimma burinsa na takarar shugaban kasa a 2027, wannan somin taɓi ne.
"Manyan kusoshin NNPP na iya fuskantar irin haka idan Kwankwaso ya ga za su zame masa barazana a burinsa na hawa mulki."

- Musa Iliyasu Kwankwaso.

Iliyasu Kwankwaso ya ba Abba mafita

Jigon wanda tsohon kwamishina ne a mulkin Ganduje ya nuna damuwa kan zubewar mutuncin Gwamma Abba matukar ya ci gaba zama karkashin ikon Kwankwaso.

Musa Iliyasu ya shawarci gwamnan Kano ya tsaya da kafarsa domin kate mutuncinsa a idon mutanen jihar.

Gwamna Abba ya bukaci a zauna lafiya

A wani rahoton kuma gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya yi kira ga Fulani su zauna lafiya da kowa a Kano musamman abokan zamansu Hausawa.

Abba ta bakin kwamishinan ayyuka na musamman, Usman Aliyu, ya buƙaci Fulani, Hausawa da sauran ƙabilu su rungumi zaman lafiya

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262