Kwankwaso Ya Share Hanyar 2027 ga Abba, Ya yi wa Siyasar APC Illa

Kwankwaso Ya Share Hanyar 2027 ga Abba, Ya yi wa Siyasar APC Illa

  • Jagoran Kwankwasiyya, Rabi'u Musa Kwankwaso ya karbi dimbin magoya bayan jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya
  • Manyan yan siyasa kusan 2,000 ne daga kananan hukumomi daban daban na jihar Kano suka dawo tafiyar jam'iyyar NNPP
  • Rabi'u Kwankwaso ya yi bayani na musamman yayin karɓar dimbin mutanen inda ya bayyana cewa za su cigaba da aiki tare

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano - Jam'iyyar NNPP mai mulki a Kano ta samu ƙarfi yayin da ta karbi dimbin mutane da suka sauya sheka.

Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ne ya karbi mutanen daga yankuna daban daban yayin da ya shiga garin Kano.

Kwankwaso
Yan APC sun koma NNPP a Kano. Hoto: Sanusi Bature D-Tofa
Asali: Facebook

Daraktan yada labaran gwamnatin Kano, Sanusi Bature Dawakin-Tofa ya bayyana yadda taron ya gudana a shafinsa na Facebook.

Kara karanta wannan

Tafiyar Kwankwasiyya ta gamu da cikas, sabon shugaban NNPP ya bayyana a Kano

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kwankwaso ya karbi masu sauya sheka

Madugun Kwankwasiyya, Rabi'u Musa Kwankwaso ya karbi mutane da dama daga kananan hukumomin Kano zuwa NNPP.

Wadanda suka sauya sheƙar sun hada da tsofaffin kansiloli 10, mutane 646 daga karamar hukumar Tofa da mutane 1,120 daga karamar hukumar Rimingado.

Manyan yan siyasa da suka sauya sheka

Bayan tarin kansiloli da suka sauya sheka zuwa NNPP akwai shugaban matasan Rimingado, Kwamared Baffa Galadima.

Haka zalika akwai shugaban jam'iyyar SDP na karamar hukumar Rimingado, Hon. Musa Dandole Dokadawa.

Bayanin Kwankwaso kan sauya sheka

Sanata Rabi'u Kwankwaso ya bayyana cewa jam'iyyar NNPP na samun karɓuwa ne saboda yadda ta ba ilimi muhimmaci.

Kwankwaso ya nuna farin ciki kan yadda NNPP ke cigaba da samun karɓuwa wajen al'umma a Najeriya.

Ana ganin hakan wata hanya ce da za ta ba Abba Kabir Yusuf samun nasara a zaben 2027 cikin sauki.

Kara karanta wannan

Wasu na gudun APC a Arewa, daruruwa sun watsar da PDP, sun bi sahun Ganduje

Abba ya sasanta rikicin NNPP

A wani rahoton, kun ji cewa gwamna Abba Kabir Yusuf ya jagoranci sasanta wani rikicin gida a jam'iyyar NNPP mai mulki a Kano.

Abba Yusuf ya yi sulhu ne tsakanin sakataren gwamnatin Kano, Dr Abdullahi Baffa Bichi da wasu jiga jigan jam'iyyar a gidan gwamnati.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng