Rikicin NNPP: Gwamna Abba Ya Juyawa Kwankwaso Baya kan Mutum 2 a Kano

Rikicin NNPP: Gwamna Abba Ya Juyawa Kwankwaso Baya kan Mutum 2 a Kano

  • Rikicin cikin gida a NNPP na neman ruguza alaƙar Abba Kabir Yusuf da Uban gidansa a siyasa, Rabiu Musa Kwankwaso
  • Wasu majiyoyi sun ce Kwankwaso ya nemi a sauke wasu mutum biyu daga muƙamansu amma Gwamna ya nuna ɓa haka ba
  • A yanzu wata kungiya ta ɓulla a Kano tana neman Abba ya daina bari Kwankwaso na juya shi, ya tsaya da kafarsa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kano - Alamu sun nuna alaƙa ta fara tsami tsakanin Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano da Mai gidansa, Dr. Rabiu Musa Kwankwaso.

Wasu majiyoyi sun bayyana cewa Gwamna Abba ya take umarnin Kwankwaso na korar wasu manyan ƙusoshin gwamnati.

Kwankwaso da Abba Kabir.
Alamu sun nuna an samu sabani tsakanin Gwamna Abba da Kwankwaso a Kano Hoto: Rabiu Musa Kwankwaso, Abba Kabir Yusuf
Asali: Facebook

Kwankwaso ya nemi Abba ya sauya mutum 2

Kara karanta wannan

Gwamna Abba ya fice daga Kano ana tsaka da rikicin jam'iyyar NNPP

PM News ta tattaro cewa waɗanda Kwankwaso ya umarci a kora sune sakataren gwamnati, Abdullahi Baffa Bichi da kwamishinan yaɗa labarai, Baba Ɗantiye.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wata majiya ta yi ikirarin cewa Kwankwaso ba ya jin daɗin zama da SSG Baffa Bichi saboda ba ya bin umarninsa wajen tafiyar da harkokin ofishinsa.

Bugu da ƙari, an ce jagoran Kwankwasiyya ya buƙaci Gwamna Abba ya maye gurbin kwamishinan yaɗa labarai da wani fitaccen ɗan soshiyal midiya.

A ganin Kwankwaso, wanda yake son a ba kwamishinan yaɗa labarai yana gogewar da zai kare gwamnatin Abba ta kowane hali.

Alaƙa ta fara tsami tsakanin Abba da Kwankwaso

To sai dai a cewar wasu majiyoyi na kusa da gwamnan, Abba Kabir Yusuf ya gwammace ya tattauna gaba-da-gaba da Kwankwaso kan batun maimakon ya yi aiki da ‘umarnin’.

A halin yanzu dai NNPP ta dare gida biyu, wata ƙungiya mai sunan "Abba tsaya da ƙafarka," ta bayyana kuma burinta gwamnan Kano ya ɓalle daga gidan Kwankwasiyya.

Kara karanta wannan

Kwankwaso ya yi magana kan rikicin NNPP a Kano, ya faɗi shawarar da ya yanke

Ƙungiyar ta ce lokaci ya yi da Gwamna Abba zai tashi daga ɗan amshin shata da wani a gefe ke juya shi yadda ya ga dama, cewar rahoton Punch.

Kwakwaso ya ƙi cewa komai kan rikicin NNPP

A wani rahoton kuma jagoran NNPP na ƙasa, Rabiu Musa Kwankwaso ya ce ba zai tsoma bakinsa a rikicin da ya ɓarke a jam'iyyar a Kano ba.

Kwankwaso ya ce bai kamata a saka shi a lamarin da bai shafe shi ba, yana mai cewa shugaban NNPP ne ke da hurumin magana.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262