'Yan Majalisar PDP Sun Rasa Kujerunsu, An Ba INEC Damar Shirya Sabon Zaɓe
- Tsagin majalisar dokokin jihar Ribas da ke goyon bayan Nyesom Wike ya bayyana kujerun ƴan majalisa huɗu a matsayin babu kowa
- Kakakin majalisar, Martin Amaewhule ya ce sun ɗauki wannan matakin ne saboda rashin halartar zaman majalisa na kwanaki 152
- Dukkan waɗanda wannan mataki ya shafa suna goyon bayan Gwamna Siminalayi Fubara a rikicin siyasar jihar Ribas
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Rivers - Majalisar dokokin jihar Ribas karkashin jagorancin Martin Amaewhule ta ayyana kujerun ƴan majalisa huɗu a matsayin waɗanda babu kowa.
Majalisar wadda ke goyon bayan ministan Abuja, Nyesom Wike ta ce ta ɗauki wannan matakin ne saboda ƴan majalisar guda hudu sun daina halartar zamanta.
Tashar Channels tv ta ce waɗanda matakin ya shafa sun haɗa da shugaban ma'aikatan gidan gwamnatin Ribas, Edison Ehie da wasu mutum uku da ke tsagin Gwamna Fubara.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shugaban majalisar dokokin, Martin Amaewhule shi ne ya sanar da haka a zaman yau Talata, 15 ga watan Oktoba, 2024 a Fatakwal, rahoton Vanguard.
Meyasa majalisa ta ɗauki wannan mataki?
Amaewhule ya ce Hon. Ehie bai sanar da majalisa sabon muƙamin da ya samu a hukumance ba, don haka aka bayyana kujerarsa a matsayin babu kowa.
Dangane da kujeurun Victor Oko-Jumbo da sauran ƴan majalisa biyu, majalisa ta kaɗa kuri'a inda a karshe ta tabbatar da kujerunsu a matsayin babu kowa saboda rashin halartar zama na tsawon kwanaki 152.
A cewar majalisar, rashin halartar zamanta na tsawon wannan lokaci ba tare da izini ba ya saɓawa kundin tsarin mulkin Najeriya.
Majalisar Ribas ta ba INEC damar cike guraben
Majalisar ta kuma amince ta rubutawa INEC takardar bada damar gudanar da zaben maye gurbin waɗannan ƴan majalisa hudu cikin kwanaki 90.
Haka nan kuma majalisar ta amince da sake bai wa Gwamna Siminalayi Fubara damar gabatar da kudurin kasafin kudin 2024 wanda kotu ta soke.
Gwamna Fubara dai ya gabatar da kasafin kuɗin 2024 gaban tsagin majalisar karkashin jagorancin Edison Ehie, amma daga bisani kotun ɗaukaka kara ta soke shi.
Gwamna Fubara ya ba Wike haƙuri
A wani labarin kuma Siminalayi Fubara ya bayyana cewa sai da ya yi kokarin ganin an kaucewa tashin hankali a jiharsa ta hanyar sulhu da Nyesom Wike
Gwamnan ya ce ya roki tsohon mai gidansa, Nyesom Wike da ya zubar da makamansa domin samun wanzuwar zaman lafiya a jihar amma ya ƙi.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng