Zaben Ondo: Gwamnan PDP Ya Yi Kira a Sauya Kwamishiniyar Zabe, Ya Fadi Dalili
- Gwamnan jihar Oyo ya miƙa sabuwar buƙata zuwa ga shugaban hukumar INEC na ƙasa kan zaɓen Ondo da za a gudanar
- Seyi Makinde ya buƙaci Farfesa Mahmud Yakubu da ya sauya kwamishiniyar INEC ta jihar Ondo, Oluwatoyin Babalola
- Makinde ya yi zargin cewa Babalola ba za ta yi adalci ba a zaɓen da za a gudanar a ranar, 16 ga watan Nuwamban 2024
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Ondo - Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde ya yi kira da a gaggauta sauya kwamishiniyar INEC ta jihar Ondo, Oluwatoyin Babalola.
Gwamna Makinde ya yi kira da a sauya Oluwatoyin Babalola ne kafin zaɓen gwamnan jihar da za a yi a ranar 16 ga watan Nuwamban 2024.
Gwamna Makinde ya ce ya yi wannan kiran ne ne domin tabbatar da cewa hukumar INEC ta zama ƴar ba ruwana a zaɓen, cewar rahoton jaridar Tribune.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnan ya yi wannan kiran ne a lokacin ƙaddamar da yaƙin neman zaɓen PDP na gwamnan Ondo wanda za a yi ranar 16 ga watan Nuwamban 2024.
Gwamna Makinde ya yi kira ga shugaban INEC
Gwamna Makinde ya buƙaci shugaban hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC), Farfesa Mahmood Yakubu da ya sauyawa Oluwatoyin Babalola wajen aiki bisa zargin nuna ɓangaranci da alaƙa da wata jam'iyyar da za ta fafata a zaɓen.
"Wannan saƙo ne ga shugaban INEC na ƙasa, Farfesa Yakubu Mahmood cewa dole ne ku sauya kwamishiniyar INEC ta Ondo, Misis Oluwatoyin Babalola, Ƴar asalin Ondo ce."
"Za mu yi zanga-zanga har sai an cire ta. Dole ne a sauya ta. A nan aka haife ta, iyayenta suna nan. Ba za ta taɓa yin adalci a wannan zaɓen ba. Ba mu son ta a jihar Ondo, dole ne Oluwatoyin Babalola ta tafi."
"Abin da suka yi a Edo ba zai yi nasara ba a Ondo. Za mu yi zanga-zanga har sai an cire ta. A kawo wanda zai yi adalci. Mu a matsayinmu na PDP ba ma tsoron a yi zaɓe. A cire ta idan ba haka ba, za mu ci gaba da yin zanga-zanga."
- Gwamna Seyi Makinde
Mambobin APC sun koma PDP a Ondo
A wani labarin kuma, kun ji cewa dubban 'yan jam’iyyar APC da ke mazaɓa ta ɗaya, a garin Ore, a ƙaramar hukumar Odigbo ta jihar Ondo, sun sauya sheƙa zuwa PDP.
Mambobin na APC sun koma PDP ne a ranar Asabar, 12 ga watan Oktoba gabanin zaɓen gwamnan jihar da za a yi a ranar 16 ga watan Nuwamba.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng