Igbo Sun Yi Nasara Lashe Kujeru a Zaben Kananan Hukumomi a Arewacin Najeriya

Igbo Sun Yi Nasara Lashe Kujeru a Zaben Kananan Hukumomi a Arewacin Najeriya

  • Bayan sanar da zaben kananan hukumomi da aka gudanar a jihar Plateau, yan kabilar Igbo biyu sun samu nasara
  • Hukumar zaben jihar, PLASIEC ta tabbatar da haka ne inda ta ba waɗanda suka yi nasara satifiket na tabbatar da su
  • Hakan ya biyo bayan sanar da sakamakon zaben da jam'iyyar PDP ta lashe duka kujerun kananan hukumomin jihar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Plateau - Hukumar zaben jihar Plateau (PLASIEC) ta samar da zaben kananan hukumomi da aka yi.

Hukumar ta ce jam'iyyar PDP ce ta yi nasarar lashe duka kujerun ƙananan hukumomi da kansiloli da aka gudanar.

Matasa a kabilar Igbo sun zama kansiloli a Arewa
An samar da zaben kananan hukumomi inda yan kabilar Igbo 2 suka samu nasara. Hoto: Caleb Mutfwang.
Asali: Facebook

Igbo sun samu kujeru a zaben Plateau

Kara karanta wannan

Wasu na gudun APC a Arewa, daruruwa sun watsar da PDP, sun bi sahun Ganduje

PLASIEC ta mika satifiket ga kansiloli 304 domin tabbatar da su a matsayin wadanda suka lashe zaben, cewar rahoton Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Daga cikinsu akwai yan kabilar Igbo guda biyu daga unguwannin Tafawa Balewa da kuma Vanderpuye duka a Jos ta Arewa.

Hon. Austin Wachukwu daga jihar Abia shi ya yi nasarar zama kansilan unguwar Vanderpuye da ke Jos ta Arewa.

Sai kuma Hon. Okoro Uzoma daga jihar Imo da zai jagoranci unguwar Tafawa Balewa duka a yankin Jos ta Arewa a jihar Plateau.

Za a sake zabe a wasu unguwannin Plateau

Yayin gabatar da satifiket din, shugaban hukumar PLASIEC, Plangji Cishak ya taya wadanda suka yi nasara murnar lashe zaben.

Cishak ya tabbatar da sake zaɓe a wasu unguwanni 21 da aka ayyana zaben wanda bai kammala ba, Vanguard ta ruwaito.

Ya ce kansilolin wannan yankin ba za su samu satifiket ba saboda rashin kammala zaben, ya ce za a gudanar da zaben a ranar 19 ga watan Oktoban 2024.

Kara karanta wannan

An shiga rudani da yan bindiga suka hallaka dan takarar APC, ana daf da zaɓe

APC ta tsira da kujera 1 a zaɓe

Kun ji cewa hukumar zaben jihar Akwa Ibom ta sanar da sakamakon zaben kananan hukumomi da aka gudanar.

Hukumar AKISIEC ta ce jam'iyyar PDP ta yi nasarar lashe duka kananan hukumomi 30 da aka gudanar a jihar.

AKISIEC ta tabbatar da cewa jam'iyyar APC mai adawa a jihar ta tsira da kujerar ƙaramar hukumar Essien Udim.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.