Gwamnan Zamfara Ya Fadi Lokacin Gudanar da Zaben Ciyamomi
- Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal ya bayyana cewa nan ba da jimawa ba za a gudanar da zaben kananan hukumomi
- Dauda ya bayyana cewa za a gudanar da zaɓen ne domin bin umarnin hukuncin da Kotun Ƙoli ta yanke kan cin gashin kansu
- Ya kuma bayyana cewa hukumar zaɓe mai zaman kanta ta jihar za ta fitar da jadawalin yadda zaɓen zai kasance
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Zamfara - Gwamnan Zamfara, Dauda Lawal, ya bayyana cewa nan ba da jimawa ba za a gudanar da zaɓukan ƙananan hukumomi.
Gwamna Dauda ya bayyana hakan ne a ranar Litinin yayin wani taron majalisar zartarwa na jihar, inda ya jaddada muhimmancin gudanar da zaɓen kananan hukumomin bisa ga hukuncin da Kotun Ƙoli ta yanke.

Asali: Twitter
Mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa a shafinsa na Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Dauda ya rantsar da shugaban hukumar zaɓe
A taron majalisar, Gwamna Dauda Lawal ya kuma rantsar da Bala Aliyu Gusau a matsayin shugaban hukumar zaɓe mai zaman kanta ta jihar Zamfara.
Wa’adin masu kula da shugabancin ƙananan hukumomin jihar 14 zai ƙare ne a ranar 23 ga watan Oktoba, 2024.
Gwamna Dauda Lawal ya ƙara da cewa a kwanakin baya ya rattaɓa hannu kan gyaran dokar zaɓen jihar Zamfara, wacce ta shafi zaɓen ƙananan hukumomi da ke tafe.
Za a yi zaɓen ciyamomi a Zamfara
"Bisa hukuncin Kotun Ƙoli na baya-bayan nan, muna buƙatar mu gudanar da zaɓe a ƙananan hukumomin mu."
"Bayan rattaɓa hannu kan dokar da aka yi wa kwaskwarima, hukumar zaɓe mai zaman kanta ta jiha za ta sanar da jadawalin zaɓen da wuri-wuri domin mu samu zaɓaɓɓun shugabannin ƙananan hukumomi a Zamfara."
- Gwamna Dauda Lawal
PDP ta lallasa APC a zaɓen ciyamomi
A wani labarin kuma, kun ji cewa jam'iyyar PDP ta samu gagarumar nasara kan APC da sauran jam'iyyun adawa a zaben kananan hukumomin jihar Filato.
Jam’iyyar PDP ta samu nasarar lashe kujerun kananan hukumomi 10 yayin da hukumar zaben Filato (PSIEC) ta fara bayyana sakamakon zaben.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng