Rabuwar PDP: Gwamnan Bauchi Ya Bayyana Makomar Rikicin da Ya Addabi Jam'iyya
- Gwamnan jihar Bauchi kuma shugaban ƙungiyar gwamnonin PDP, Bala Mohammed ya ce an warware rikicin jam'iyyarsu
- Bala ya bayyana cewa gwamnonin PDP da sauran masu ruwa da tsakin jam'iyyar ne suka cimma matsayar kawo zaman lafiya
- Ya ƙara da cewa an ɗage dakatarwar da dukkanin ɓangarorin kwamitin NWC guda biyu suka yi wa junansu a makon jiya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Shugaban ƙungiyar gwamnonin PDP kuma gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya yi magana kan rikicin da ya dabaibaye jam'iyyar.
Bala Mohammed ya bayyana cewa gwamnonin PDP sun sasanta rikicin samun ɓangarori da ya shafi kwamitin gudanarwa na jam’iyyar na ƙasa (NWC).
Jaridar The Punch ta rahoto cewa ya bayyana haka ne a ranar Talata a lokacin da yake zantawa da manema labarai a babban filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe da ke Abuja.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Me Gwamna Bala ya ce kan rikicin PDP?
Gwamna Bala ya bayyana cewa gwamnonin PDP da sauran masu ruwa da tsaki a jam'iyyar ne suka cimma matsayar warware rikicin, rahoton The Nation ya tabbatar.
"Rikicin ya ƙare. Gwamnoni, kwamitin amintattu, da sauran masu ruwa da tsaki sun yanke shawarar cewa ya kamata kwamitin NWC ya koma matsayin da ya ke. Yanzu sun haɗe."
- Gwamna Bala Mohammed
Gwamnan tare da rakiyar shugaban riƙo na ƙasa, Umar Damagum yayin da yake tafiya jihar Ondo domin gudanar da yaƙin neman zaɓen gwamna na jam’iyyar PDP, ya bayyana cewa an ɗage dakatarwar da ɓangarorin biyu suka yi.
Shugaban jam'iyyar PDP ya yi ƙarin haske
Da yake tofa albarkacin bakinsa Umar Damagum ya tabbatar da cewa rikicin da ya addabi jam'iyyar ya ƙare.
"Jam’iyyar ta haɗe, kuma babu wani ɗan kwamitin NWC da aka bari a baya."
- Umar Damagum
Gwamnonin PDP sun faɗi shugaban jam'iyya
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnonin da aka zaba a karkashin inuwar PDP sun soke dakatarwar da aka yi wa mukaddashin shugaban jam’iyyar na kasa, Umar Damagum.
Shugaban ƙungiyar gwamnonin kuma gwamnan Bauchi, Gwamna Bala ya ce a halin yanzu sun amince kowa ya zauna a matsayinsa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng