Yadda Abba Ya Kashe Wata Wutar Rikicin da aka Kunna Masa a Kano

Yadda Abba Ya Kashe Wata Wutar Rikicin da aka Kunna Masa a Kano

  • Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya dauki matakin sasanta jiga jigan jam'iyyar NNPP da suka samu sabani a kan siyasa
  • Rahotanni sun nuna cewa an sasanta rikicin ne a ofishin gwamna Abba Kabir Yusuf a fadar gwamnatin jihar a daren Litinin
  • An ruwaito cewa daga cikin jiga jigan NNPP da suka samu sabani akwai sakataren gwamnatin Kano, Abdullahi Baffa Bichi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano - Gwamantin Kano karkashin Abba Kabir Yusuf ta dauki matakin sasanta rikicin cikin gida da ya barke a NNPP.

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya sasanta sakataren gwamnatin jihar da wasu manyan yan jam'iyyar NNPP.

Kara karanta wannan

Wasu na gudun APC a Arewa, daruruwa sun watsar da PDP, sun bi sahun Ganduje

Abba Kabir
Abba ya yi sulhu a Kano. Hoto: Abba Kabir Yusuf
Asali: Facebook

Legit ta gano yadda zaman ya gudana ne a cikin wani sako da Sanusi Bature Dawakin-Tofa ya wallafa a Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yan NNPP masu rikici a jihar Kano

Rahotanni sun nuna cewa manyan da suka samu sabani sun hada da sakataren gwamnatin Kano da dan takarar karamar hukumar Bichi.

Abba Kabir Yusuf ya kira sakataren gwamnati, Dr Abdullahi Baffa da dan takarar ƙaramar hukumar Bichi, Hamza Sule Maifata domin sulhu.

Baffa Bichi ya yarda da zaman sulhu

Bayan zama da Abba Kabir Yusuf, Dr Abdullahi Baffa Bichi ya ce komai ya wuce tsakaninsa da wadanda suka samu sabani.

Dr Abdullahi Baffa ya ce za su cigaba da bin duk wani abin da gwamna Abba Kabir Yusuf ya kawo domin cigaban jihar Kano

Maifata ya ce sun yafewa juna bayan sulhu

Kara karanta wannan

Kano: Bichi ya maida martani kan zargin neman farraka Abba da Kwankwaso

A daya bangaren, Hamza Sule Maifata ya ce bayan zaman sun fahimci cewa masu yada jita jita ne suka nemi kunna wuta a tsakaninsu.

Maifata ya jaddada cewa sun yafewa juna kuma za su cigaba da aiki tare kamar yadda suka saba a baya domin kawo cigaba a Kano.

Kakakin majalisar dokokin jihar Kano na cikin waɗanda suka halarci zaman sulhun a daren Litinin.

Abba tsaya da kafarka: Bichi ya wanke kansa

A wani rahoton, kun ji cewa sakataren gwamnatin Kano ya ya bayyana cewa ba shi da hannu kan kokarin raba Abba Kabir Yusuf da Rabi'u Kwankwaso.

Dr Abdullahi Baffa Bichi ya ce sam ba shi da alaka da mutanen da suka kirkiro maganar 'Abba tsaya da kafarka' a Kano.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng