Wasu na Gudun APC a Arewa, Daruruwa Sun Watsar da PDP, Sun bi Sahun Ganduje
- Daruruwan ƴa ƴan jam'iyyar PDP a jihar Nasarawa sun gaji da ita, sun kama layin APC mai mulkin Najeriya
- Rahotanni sun tabbatar da cewa akalla mambobi 600 ne da sauran yan jam'iyyar SDP suka koma APC
- Kwamishinan muhalli da albarkatu, Yakubu Kwanta ya karbi tubabbun a gundumar Ningo Bohar a Akwanga
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Nasarawa - Jam'iyyar PDP a Najeriya ta sake samun matsala bayan sauya shekar daruruwan mambobinta.
Akalla mambobin PDP 600 suka watsar da ita zuwa jam'iyyar APC mai mulki a jihar Nasarawa.
Yan PDP 600 sun koma jam'iyyar APC
Leadership ta ruwaito cewa mambobin PDP sun sauya sheka ne a gundumar Ningo Bohar da ke karamar hukumar Akwanga.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kwamishinan muhalli da albarkatun kasa, Yakubu Kwanta shi ya karbi sababbin tuban zuwa APC.
Daga cikin wadanda aka karban akwai yan SDP da sauran jamiyyu yayin bikin bude ofis a Ningo, cewar rahoton The Sun.
Kwanta ya yabawa yan yankin kan irin goyon baya da suke ba gwamnatin jihar Nasarawa da kuma jam'iyyar APC.
Ya kuma shawarci alumma da su fito domin nunawa APC gata a zaben kananan hukumomi da za a gudanar.
Dan Majalisa ya yabawa Gwamna Sule
Dà yake magana, mai tsawatarwa a Majalisar jihar Nasarawa, Larry Ven-Bawa ya yabawa Gwamna Abdullahi Sule da kwamishinan kan ayyukan alheri da suke yi.
Ven-Bawa da ke wakiltar Akwanga ta Arewa ya ce zai yi kokarin kwaikwayon gwamnan da kuma kwamishinan wurin samar da abubuwan more rayuwa ga yankin.
Isaac Fayose ya ayyana kansa shugaban PDP
A wani labarin, kun ji cewa rigimar jam'iyyar PDP ta sauya salo bayan kanin tsohon gwamnan Ekiti, Ayodele Fayose ya ayyana kansa a matsayin shugabanta.
Kanin tsohon gwamnan Ekiti mai suna Isaac Fayose ya ce daga yau shi ne shugaban PDP, duk wanda ba yarda ba ya je kotu.
Hakan ya biyo bayan rikicin da ya barke a PDP da ke neman raba ta gida biyu bayan tsaginta ya dakatar da shugabanta, Umar Damagum.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng