'Za Su Hana Tinubu Takara a 2027?’ Kusa Ya Dura kan Masu Sukar Atiku
- Jigo a PDP, Dele Momodu ya yi maratani kan yan siyasar da suka fara maganar cewa bai kamata Atiku Abubakar ya yi takara ba a 2027
- Momodu ya ce idan maganar shekaru ne, to Bola Tinubu ya kamata a fara tunkara da maganar rashin tsayawa takara a zaɓen 2027 ba Atiku ba
- Tsohon gwamnan Ekiti, Ayodele Fayose ne ya yi kira da cewa bai kamata Atiku Abubakar ya tsaya takara a zabe mai zuwa ba kwata kwata
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Jigo a PDP kuma tsohon dan takarar shugaban ƙasa, Dele Momodu ya yi maratani ga masu sukar takarar Atiku a 2027.
Dele Momodu ya ce ba wanda yake da hurumin hana Atiku Abubakar tsayawa takara a zaɓen 2027.
Legit ta tatttaro bayanan Dele Momodu ne a cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook a ranar Litinin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Dele Momodu: 'Atiku zai iya takara a 2027'
Dele Momodu ya ce matuƙar Atiku Abubakar yana cikin koshin lafiya ba wanda ya isa ya hana shi tsayawa takara a zaɓen 2027.
Sai dai dan siyasar ya ce mutane suna da yancin kin zabensa amma ba za su iya hana shi tsayawa takara ba kwata kwata.
Za a hana Tinubu takara a 2027?
Dele Momodu ya ce idan wasu sun ce Atiku ya tsufa to sai su fara fadin haka ga Bola Tinubu domin shi ya fi cancanta a fadawa hakan.
Sannan ya kara da cewa idan tsufa suke gudu da ba su marawa Tinubu baya ba a 2023, ya ce da za a gansu ne a bayan masu karancin shekaru.
Momodu ya ce Atiku na da nagarta
Dele Momodu ya ce Atiku ya nuna nagarta a dimokuraɗiyyance ta inda bai nuna iko da mallaka a wata jiha ba a fadin ƙasar nan.
Ya ce Atiku ya kafa kasuwanci bayan gama mulki wanda duk masu sukarsa sun gaza yin hakan, a cewar Momodu wannar alama ce ta nagarta a tattare da Atiku.
APC ta yi magana kan tsarin Tinubu
A wani rahoton, kun ji cewa APC ta yi martani kan kira da ake yi ga Bola Tinubu ya canza tsare tsarensa saboda matsalar tattalin arziki.
Daraktan yada labaran APC na kasa, Bala Ibrahim ne ya fitar da sanarwar a ranar Juma'a inda ya ce suna kan gyara ne a Najeriya.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng