An Gano Gwamnonin PDP da Ke Son Tsige Damagum, An Gaza Cimma Matsaya

An Gano Gwamnonin PDP da Ke Son Tsige Damagum, An Gaza Cimma Matsaya

  • An tashi daga taron gwamnonin jam'iyyar PDP ba tare da cimma nasara kan yanke matsayar Umar Damagum a NWC ba
  • Wasu a PDP na ganin rashin dacewar Ambasada Damagum ya cigaba da zama shugaban jam'iyyar PDP, hakan ya jawo baraka
  • Mafi akasarin gwamnonin na son Damagum ya koma tsohon mukaminsa na mataimaki shugaban PDP lokacin Iyorchia Ayu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT, Abuja - Da alama dai tsuguno ba ta kare ba, yayin da gwamnonin PDP su ka gaza samun matsaya a kan makomar shugaban PDP, Umar Iliya Damagum.

Rikicin cikin gida da ya ke addabar jam'iyyar ya samar da rarrabuwarta, inda aka samu tsagin da ya fitar da sabon shugaba, Yayari Mohammed.

Kara karanta wannan

Rabuwar PDP: Gwamnan Bauchi ya bayyana makomar rikicin da ya addabi jam'iyya

Adawa
Gwamnonin PDP sun gaza cimma matsaa kan Damagum Hoto: @OfficialPDPNig
Asali: Twitter

Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa an samu rarrabuwar kai tsakanin gwamnonin, inda wasu ke goyon bayan a bar Ambasada Damagum ya cigaba da shugabanci, wasu kuma su ka ki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnonin PDP da su ka goyi bayan Damagum

Wasu daga cikin gwamnonin PDP sun bayyana cewa ya dace a bar Ambasada Umar Iliya Damagum ya cigaba da shugabanci na wani lokaci kafin a daidaita.

Gwamnonin sun hada da Seyi Makinde na jihar Oyo da gwamna Ahmadu Fintiri na jihar Adamawa, Agbu Kefas na jihar Taraba da kuma gwamnan Filato, Caleb Mutfwang .

Wasu gwamnonin PDP na son tsige Damagum

Rahotanni sun ce gwamna Bala Mohammed na Bauchi da Godwin Obaseki na Edo, Siminalayi Fubara na Rivers, gwamnan Osun Ademola Adeleke da Sheriff Oborevwori na Delta ba su goyi bayan Damagum ba.

Sauran ggwamnonin da ke son a cire Damagum daga shugabancin jam'iyyar sun hada da Douye Diri na Bayelsa, Umo Eno na Akwa Ibom su ka bukaci Damagum ya koma tsohon mukaminsa.

Kara karanta wannan

Gwamnonin PDP sun raba gardama, sun sanar da sahihin shugaban jam'iyya na ƙasa

Rikicin jam'iyyar PDP ya kara kamari

A wani labarin kun ji cewa barakar da PDP ta samu ta kara kamari bayan tsagin da ke adawa da shugabancin Ambasada Umar Damagum ya fitar da sabon shugaba duk da kotu ta dakatar da haka.

Yayari Mohammed, ya bayyana cewa tuni ya fara aiki a matsayin shugaban jam'iyya da wani tsagi na kwamitin gudanarwar jihar ya nada, tare da alkawarin zai yi aiki da adalci.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.