Kano: Bichi Ya Maida Martani kan Zargin Neman Farraka Abba da Kwankwaso
- Yayin da ake zargin Baffa Bichi da neman raba Rabiu Kwankwaso da Abba Kabir, sakataren gwamnatin Kano ya magantu
- Sakataren gwamnatin ya musanta alaka da kungiyar da ake zargin yana daukar nauyinta ta 'Abba tsaya da kafarka' a Kano
- Bichi ya ce kwata-kwata bai da alaka da ita kuma bai santa ba inda ya ce yana mutunta Gwamna Abba Kabir a matsayin mai gidansa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kano - Sakataren gwamnatin jihar Kano, Abdullahi Baffa Bichi ya yi magana kan zarginsa da ake yi.
Bichi ya nisanta kansa daga zargin neman farraka Gwamna Abba Kabir da mai gidansa, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.
Ana zargin neman raba Abba da Kwankwaso
Sakataren gwamnatin ya fadi haka ne bayan ganawa da Abba Kabir kan zargin kafa kungiyar 'Abba tsaya da kafarka', cewar Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hakan ya biyo bayan zargin Bichi da daukar nauyin kungiyar da ke son Abba Kabir ya zama mai gashin kansa game da mukin jihar Kano.
Ana zargin tun bayan hawan Gwamna Abba Kabir jagora Kwankwaso ke cigaba da juya alakar gwamnatin jihar yadda yake so, kamar yadda Freedom Radio ta wallafa.
Bichi da zargin neman raba Abba da Kwankwaso
A martaninsa, Bichi ya ce ba shi da alaka ta kusa ko nesa da kungiyar da ake zarginsa a kai.
"Gwamna Abba mai gida na ne, tuntuni na mika kaina gare shi da ayyuka na, duk abin da yake so shi nake yi masa."
"Wannan kungiya da ake alakanta ni da ita, ban san ta ba kuma ba ni da wata alaƙa da ita."
- Abdullahi Baffa Bichi
NNPP ta dakatar da Bichi a Kano
Kun ji cewa rikici ya ɗauki sabon salo a NNPP a Kano da aka dakatar da sakataren gwamnatin jiha, Abdullahi Baffa Bichi da kwamishinan sufuri.
Shugaban NNPP na jihar, Hashim Sulaiman Dungurawa ya ce sun dakatar da manyan ƙusoshin biyu kan rashin ladabi ga jam'iyya.
Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da rikici ke neman raba kawunan manyan ƙusoshin NNPP mai mulkin Kano.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng