Rigima Ta Ɓarke a NNPP, An Dakatar da Sakataren Gwamnatin Kano da Kwamishina

Rigima Ta Ɓarke a NNPP, An Dakatar da Sakataren Gwamnatin Kano da Kwamishina

  • Rikici ya ɗauki sabon salo a NNPP a Kano da aka dakatar da sakataren gwamnatin jiha, Abdullahi Baffa Bichi da kwamishinan sufuri
  • Shugaban NNPP na jihar, Hashim Sulaiman Dungurawa ya ce sun dakatar da manyan ƙusoshin biyu kan rashin ladabi ga jam'iyya
  • Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da rikici ke neman raba kawunan manyan ƙusoshin NNPP mai mulkin Kano

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Kano - Rikici ya ƙara tsananta a jam'iyya mai mulkin Kano, NNPP ta dakatar da sakataren gwamnatin jiha, Abdullahi Baffa Bichi.

Haka nan kuma NNPP ta dakatar da kwamishinan sufuri, Muhammad Diggol kan zargin rashin ladabi da biyayya ga jam'iyyar.

Gwamna Abba Kabir Yusuf.
NNPP ta dakatar da sakataren gwamnatin Kano da kwamishinan sufuri Hoto: Abba Kabir Yusuf
Asali: Twitter

Shugaban NNPP na Kano, Hashim Sulaiman Dungurawa ne ya tabbatar da ɗaukar wannan mataki ga jaridar Daily Trust ranar Litinin.

Kara karanta wannan

Babban jigo a Kano ya zuga Gwamna Abba, ya soki tsarin Rabiu Kwankwaso

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Meyasa NNPP ta ɗauki wannan mataki?

Tun farko dai an ji Hashin Dungurawa ya sanar da dakatar da manyan ƙusoshin biyu daga NNPP a wani faifan sauti da ya karaɗe shafukan sada zumunta.

Ya ce sun ɗauki matakin dakatar da Abdullahi Baffa Bichi da kwamishinan sufuri saboda rashin ladabi, amfani da ƙarfin mulki da yunkurin ta da rikici a NNPP.

Kano: Rikici ya ɗauki sabon salo a NNPP

"Mun dakatar da sakataren gwamnatin jiha watau SSG Abdullahi Baffa Bichi da kwanishinan sufuri, Muhammad Diggol bisa keta dokar aikin ofis da rashin ladabi ga NNPP.
"Muna ƙara jinjinawa shugabannin jam'iyya na gundumomi da ƙaramar hukumar da suka fito bisa kawo mana korafin abin da ke wakana, dukkansu ƴan yankin Bichi ta Arewa ne.
"A matsayin shugabannin jiha, mun zauna kuma mun amince da cewa dakatar da su ne matakin da ya kamata a ɗauka har sai an kammala bincike."

Kara karanta wannan

Gwamna Abba ya fice daga Kano ana tsaka da rikicin jam'iyyar NNPP

- Hashim Sulaiman Dungurawa.

Bayanai sun nuna cewa rikici ya ɓarke har an fara nuna yatsa tsakanin wasu daga cikin masu ruwa da tsakin NNPP a yankin karamar hukumar Bichi, Channels tv ta kawo.

Ƴan NNPP na zargin akwai wata a kasa

Wani jigon NNPP ya shaidawa Legit Hausa cewa wasu bara gurbi a jam'iyyar waɗanda ake zargin sun karɓo kwangila ne suka fara kokarin ruguza Kwankwasiyya.

Baba Shehu ya ce wannan abubuwan da ke faruwa a NNPP shiryayye ne, kuma burinsu shi ne su sa Gwamna ya bijirewa Kwankwaso.

"Waɗanda ke kitsa wannan makircin suna can Abuja, Kano ta tsole masu ido kuma ta Allah ba ta su ba, ina tabbatar maka da cewa Mai gida zai shawo kan komai," in ji shi.

NNPP ta rasa ƴar uwar Baffa Bichi

A wani labarin NNPP ta yi babban rashi a jihar Kano yayin da 'yar uwar sakataren gwamnatin jihar Kano (SGG), Dakta Baffa Bichi ta koma APC.

Kara karanta wannan

Kwankwaso ya yi magana kan rikicin NNPP a Kano, ya faɗi shawarar da ya yanke

Hajiya Lami Bichi tare da tawagarta sun hakura da tafiyar Kwankwasiyya inda suka gana da Sanata Barau Jibrin domin su sauya-sheka.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262