Shugaban Tsagin NNPP Ya 'Kori' Kwankwaso, Ya Bukaci Ladabtar da Abba

Shugaban Tsagin NNPP Ya 'Kori' Kwankwaso, Ya Bukaci Ladabtar da Abba

  • An kara samun rikici tsakanin wasu 'ya'yan NNPP a Najeriya da jagoran jami'yyar, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso
  • Lamarin ya faru ne a jihar Neja yayin da shugaban tsagin jam'iyyar, Dr Gilbert Agbo ya jagoranci taron adawa da Kwankwaso
  • Shugaban Kwankwasiyya na jihar Neja, Danladi Umar Abdulhamid ya yi martani ga Dr Gilbert Agbo kan lamarin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Niger - Shugaban tsagin jam'iyyar NNPP, Dr Gilbert Agbo ya jagoranci zanga zangar adawa da Rabi'u Musa Kwankwaso.

Dr Gilbert Agbo ya ce Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso korarre ne daga cikin jam'iyyar NNPP a Najeriya.

Kwankwaso
Shugaban tsagin NNPP ya bukaci a kori Kwankwaso. Hoto: Abba Kabir Yusuf
Asali: Facebook

Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa shugaban kwankwasiyya a Neja ya ce har yanzu Sanata Kwankwaso ne jagoran NNPP a Najeriya.

Kara karanta wannan

Mutane 16 ‘yan gida 1 da suka shiga fagen siyasa kuma suka shahara a Najeriya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaban tsagin NNPP ya kori Kwankwaso

Mai ikirarin zama shugaban NNPP a Najeriya, Dr Gilbert Agbo ya ce dakatar da Kwankwaso da aka yi a NNPP ya nuna shi ba dan jami'yyar ba ne a yanzu.

Dr Gilbert Agbo ya fadi haka ne yayin da ya jagoranci kona jajayen huluna a sakatariyar NNPP a jihar Neja.

Dr Agbo ya bukaci a ladabtar da Abba a NNPP

Haka zalika Dr Gilbert Agbo ya bukaci NNPP ta ladabtar da gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf.

Dr Gilbert Agbo ya ce dole za a ladabtar da Abba Kabir Yusuf kan yadda ya fifita Sanata Kwankwaso a kan ra'ayin NNPP.

Kwankwasiyya ta yi raddi ga Dr Agbo

Wani shugaban Kwankwasiyya a jihar Neja ya ce maganar Dr Gilbert Agbo ba ta kan layi kwata kwata.

Danladi Umar Abdulhamid ya tabbatar da cewa har yanzu Kwankwaso ne jagoran NNPP a Najeriya kuma Dr Ahmed Ajuji ne ingantaccen shugaban jam'iyyar.

Kara karanta wannan

Shugaban kamfanin NNPCL, Kyari ya yi babban rashi, Kashim Shettima ya jajanta

Ana neman Abba ya bijirewa Kwankwaso

A wani rahoton, kun ji cewa wasu ‘yan siyasa daga jam’iyyu dabam-dabam sun fara kira ga Abba Kabir Yusuf ya tsaya a kan kafafunsa da kyau.

Masu wannan raji sun kira kungiyarsu da Abba tsaya da kafarka da nufin ceto jihar Kano daga hannun Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng