Jam'iyyar APC Ta Samu Koma Baya Ana Dab da Zaben Ciyamomi a Kano

Jam'iyyar APC Ta Samu Koma Baya Ana Dab da Zaben Ciyamomi a Kano

  • Jam'iyyar APC mai adawa a Kano ta gamu da koma baya yayin da ake shirin gudanar da zaɓen shugabannin ƙananan hukumomi
  • Sama da mambobin jam'iyyar APC guda 1,000 sun sauya sheƙa zuwa NNPP mai mulki a ƙananan hukumomin Tofa da Ghari
  • Shugaban NNPP na Kano, Dakta Hashimu Dungurawa ya yi wa masu sauya sheƙar maraba zuwa cikin jam'iyya mai kayan marmari

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kano - Jam'iyyar APC mai adawa a jihar Kano ta samu koma baya yayin da mambobinta suka sauya sheƙa zuwa NNPP mai mulki.

Sama da mambobin jam’iyyar APC guda 1,000 ne suka sauya sheka zuwa jam’iyyar NNPP mai mulki a jihar Kano.

Kara karanta wannan

Sukar Tinubu: Kalaman sanatan APC na neman kara sanya shi cikin matsala

Mambobin APC sun koma NNPP a Kano
Mambobin APC sun sauya sheka zuwa NNPP a Kano Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Jaridar Vanguard ta rahoto cewa masu sauya sheƙar sun koma NNPP ne a ƙananan hukumomin Tofa da Ghari.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mambobin APC sun koma NNPP a Kano

Bayan ficewarsu daga APC masu sauya sheƙar sun koma jam’iyyar NNPP a hukumance, rahoton jaridar PM News ya tabbatar da haka.

Shugaban jam’iyyar NNPP na jiha Dakta Hashimu Suleiman Dungurawa ne ya tarbe su a yayin wani taro da aka gudanar a ƙananan hukumomin biyu.

An gudanar da taron ne domin ƙaddamar da yaƙin neman zaɓen shugabannin ƙananan hukumomi na jam’iyyar NNPP gabanin zaɓen da ke tafe.

Daga cikin fitattun waɗanda suka halarci taron akwai ƴan takarar jam’iyyar NNPP, na ƙananan hukumomin Tofa da Ghari, Yakubu Ibrahim Adis da Hashimu Mai Sabulu.

Dukkanin ƴan takarar biyu sun bayyana ƙwarin gwiwa kan yadda jam’iyyar NNPP ke kara karfi a yankin, musamman tare da kwararowar sababin mambobi.

Kara karanta wannan

Jagora a APC ya yabi ministan Tinubu, ya fadi nasarorin da ya samu

Jigo a jam'iyyar NNPP ta koma APC

A wani labarin kuma, kun ji cewa Hajiya Lami, wata kanwar sakataren gwamnatin jihar Kano (SGG), Dakta Baffa Bichi ta fice daga jam’iyyar NNPP zuwa APC mai mulki a kasa.

Mai fafutukar mata a Kano, Hajiya Lami ta bayyana ficewa daga NNPP a gidan mataimakin shugaban majalisar dattawa Sanata Barau I Jibrin da ke babban birnin tarayya Abuja.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

iiq_pixel