Reshe Ya Juye da Mujiya: Shugaban APC Ya Shiga Matsala bayan Dakatar da Minista

Reshe Ya Juye da Mujiya: Shugaban APC Ya Shiga Matsala bayan Dakatar da Minista

  • Shugabannin APC a gundumar Toru-Ndoro da ke karamar hukumar Ekeremor sun dakatar da shugaban jam'iyyar
  • Shugabannin sun dauki matakin ne kan Eniekenemi Mitin bayan dakatar da karamin Ministan mai, Heineken Lokpobiri daga jam'iyyar
  • Wannan na zuwa ne bayan dakatar da Lokpobiri da Mitin ya yi kan zargin zangon-kasa ga jam'iyyar kwanaki biyu da suka wuce

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Bayelsa - Kwanaki biyu bayan dakatar da Ministan Bola Tinubu, shugaban APC ya shiga matsala.

Shugabannin APC a Toru-Ndoro da ke karamar hukumar Ekeremor sun dakatar da shugabanta, Mr Eniekenemi Mitin.

Shugaban APC ya shiga matsala bayan dakatar da Ministan Tinubu
An dakatar da shugaban APC bayan korar Minista a jam'iyyar. Hoto: Heineken Lokpobiri.
Asali: UGC

Yadda aka dakatar da Minista daga APC

Vanguard ta ruwaito cewa shugabannin jam'iyyar sun dauki matakin ne bayan Mitin ya dakatar da karamin Ministan mai, Heineken Lokpobiri.

Kara karanta wannan

Likitoci, lauyoyi sun nemi Tinubu ya warware matakin NNPCL da fetur ya kai N1030

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mitin ya dakatar da Lokpobiri da wasu jiga-jigan jam'iyyar kan zargin yi wa APC zangon-kasa da neman hada rikici a cikin jam'iyyar.

Sai dai shugabannin jam'iyyar a gundumar Toru-Ndoro sun bukaci al'umma su yi watsi da shugabancin Mitin saboda a yanzu ba shi ne shugabanta ba.

Suka ce sun dakatar da Mitin ne kan zargin cin amanar APC da kawo rarrabuwa da kuma baba-kere a sha'anin jam'iyyar.

Karanta labarai da ke da alaka da APC:

Tsagin PDP ya nada sabon shugaban jam'iyyar

Mun baku labarin cewa tsagin PDP ya nada sabon shugaban jam'iyyar bayan dakatar da Umar Damagum daga shugabancinta.

Kara karanta wannan

Kanin tsohon gwamna ya ayyana kansa shugaban PDP, ya kori Atiku, Wike da sauransu

Jam'iyyar ta nada tsohon shugaban ma'aikatan gwamnatin jihar Gombe, Ahmed Yayari Mohammed a matsayin shugaban jam'iyyar na rikon kwarya

Hakan ya biyo bayan barkewar rikicin cikin gida da ya daidaita jam'iyyar PDP gida biyu a yan kwanakin nan wanda har yanzu ake kai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.