An Shiga Rudani da Yan Bindiga Suka Hallaka Dan Takarar APC, Ana Daf da Zaɓe
- Ana shirin gudanar da zaben kananan hukumomi a Ogun, yan bindiga sun hallaka dan takarar APC a jihar
- Maharan sun kashe Adeyinka Adeleke ne a yankin Jide Jones da ke karamar hukumar Abeokuta ta Kudu
- Lamarin ya faru ne a yau Asabar 12 ga watan Oktoban 2024 yayin da ake shirin zaben a ranar 16 ga watan Nuwambar 2024
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Ogun - Wasu yan bindiga sun hallaka dan takarar kansila na jam'iyyar APC a jihar Ogun da ke Kudancin Najeriya.
Maharan sun yi ajalin Adeyinka Adeleke a yanki Jide Jones da ke karamar hukumar Abeokuta ta Kudu.
Yan bindiga sun hallaka dan takarar APC
Punch ta ruwaito cewa marigayin na daga cikin masu neman takara a zaɓen kananan hukumomi da za a yi watan Nuwamba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Maharan sun dira a yankin ne a cikin mota mai bakin gilashi kafin suka fara karbi ta ko ina.
Rahotanni sun tabbatar da cewa yan bindiga sun tunkari dan takarar inda suka harbe shi tare da tsallake shi su wuce.
Marigayin na neman takarar kansila a gundumar Ibara 15 a zaɓen da za a yi a ranar 16 ga watan Nuwambar 2024.
Wane martani rundunar yan sanda ta yi?
Har zuwa lokacin tattara wannan rahoto, rundunar yan sanda a jihar Ogun ba ta yi martani kan abin takaicin da ya faru ba.
Sai dai wani babban jami'in dan sanda da ya boye sunansa ya tabbatar da kisan dan siyasar a yau Asabar 12 ga watan Oktoban 2024.
"Tabbas an hallaka dan siyasar kuma iyalansa sun yanke shawarar dauke gawarsa domin yi mata sutura."
- Cewar wani dan sanda
Yan bindiga sun hallaka dan takarar PDP
Kun ji cewa wasu ‘yan bindiga sun yi ajalin wani dan takarar karamar hukuma a jihar Enugu da ke Kudancin kasar, Hon. Ejike Ugwueze.
Marigayin ya gamu da ajalinsa ne yayin da yake kan hanyar Neke Odenigbo da ke karamar hukumar Enugu ta Gabas a jihar.
Rundunar ‘yan sanda a jihar ta bakin kakakinta, DSP Daniel Ndukwe ta tabbatar da faruwar lamarin a ranar Asabar 8 ga watan Yunin 2024.
Asali: Legit.ng