Hadimin Atiku Ya Gama Bayanin Yadda Za a Sasanta Rikicin PDP, Lissafi Ya Watse a Ranar

Hadimin Atiku Ya Gama Bayanin Yadda Za a Sasanta Rikicin PDP, Lissafi Ya Watse a Ranar

  • Da alama jam’iyyar PDP za ta dogara da NEC wajen sauke duka shugabannin da ke majalisar gudanarwa ta NWC
  • Ana so majalisar kolin jam’iyyar ta umarci masu rike da mukamai a matakin kasa su yi murabus domin a nada wasu
  • Idan an dace, za a nada shugabannin rikon kwarya da za su shirya zabe, ko da an ji kotu ta na neman ta kawo cikas

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Lagos - Demola Rewaju wanda ya na cikin masu taimakawa Atiku Abubakar ya yi magana game da rikicin jam’iyyar PDP.

Mai taimakawa ‘dan takaran na PDP a zaben 2023 a harkokin sadarwa na zamani ya hango karshen rigimar jam’iyyar adawar.

A PDP
Ana kokarin magance rigimar shugabancin jam'iyyar PDP Hoto: @OfficialPDPNigeria
Asali: Twitter

Rikicin cikin gidan PDP zai zo karshe

Kara karanta wannan

Atiku ya amince gwamnan Bauchi ya zama dan takarar shugaban kasa na PDP a 2027?

A shafinsa na X, Demola Rewaju ya nuna cewa rikicin cikin gidan da ya dabaibayewa jam’iyyar PDP ya kusa zuwa karshe yanzu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

‘Dan siyasar yake cewa majalisar zartarwa watau NEC za ta tsoma baki a samu mafita.

A cewarsa, a ranar 24 ga watan Oktoba ne ‘yan majalisar NEC za su bukaci daukacin ‘yan majalisar NWC da su yi murabus.

Da zarar sun yi murabus, sai a nada shugabannin wucin-gadi a kwamitin rikon kwarya.

Wannan kwamitin rikon kwarya ne ake sa ran zai gudanar da zaben shugabanni na kasa a shekara mai zuwa watau 2025.

Idan komai ya tafi daidai, NEC wanda ita ce majalisar koli za ta fito da yadda za a yi rabon mukaman shugabanni a NWC.

Ya gama jawabinsa ya na yabawa kwarewar ‘yan siyasa kenan sai aka ji lamarin ya canza.

Kara karanta wannan

Sanata Buba da aka alakanta da 'yan bindiga zai fito takarar gwamnan Bauchi?

Kotu ta batawa 'yan jam'iyyar PDP shiri

Mista Demola Rewaju bai dade da wannan magana ba sai aka ji wata kotun tarayya ta haramta tsige Umar Iliyasu Damagum.

Wasu ‘yan PDP su na zargin cewa shugaban jam’iyya na kasa, Ambasada Umar Damagum ya na tare ne da Nyesom Wike.

A kokarin ganin bayan Nyesom Wike ne ake so a ruguza majalisar gudanarwar PDP.

Rikicin PDP ya ki jin magani

Sanata Shehu Sani ya lissafo rigingimu shida da suka dabaibaye sassan kasar nan, an ji cewa a ciki ya ambaci rikicin PDP NWC.

Tsohon sanatan ya ce mutane sun gaza shawo kansu, an mika lamarin ga Allah SWT ya magance rigingimun da suka addabi kasar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng